Abunda ya kamata ku sani game da sabon Minista Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami
Dr Isa Ali Ibrahim Pantami an haife shi ranar 20 ga watan oktoba shekarar 1972 a yankin Pantami na Gombe a tsohuwar Jihar Arewa maso gabashin Najeriya, da’ ga Malama Amina Umar Aliyu da Malam Ali Ibrahim Pantami.
Ya fara karatun tsangaya domin hardace Al-Qur’ani. Daga bisani ya shiga makarantar Firamare ta Pantami inda ya samu shaidar kamala firamare, sai kuma ya tafi makarantar sakandaren Gwamnati ta kimiya a Gombe in da ya samu shaidar kammala karatun sakandare (SSCE).
Daga nan ya wuce zuwa Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) dake Bauchi inda ya samu kwalin Digirin Fasaha na na’ura mai kwakwalwa a shekarar 2003 bayan nan yayi Digirin mataki na biyu a shekarar 2008, kafin yayi digirin digir gir (PhD) a Jami’ar Robert Gordon, Aberdeen Scotland.
Sheikh Isa Ali Pantami, kamar yadda akafi sanin shi, ya fara aiki a Jami’ar ATBU, Bauchi inda ya koyar da ilimin fasahar na’ura mai kwakwalwa kafin ya koma aiki da Jami’ar Musulunci dake Madinah a matsayin shugaban Fasahar rubutu a shekarar 2014.
KARANTA WANNAN: Kaduna, Kano, Bauchi da wasu jahohi 4 dake da ministoci 2 a gwamnatin Buhari
A shekarar 2016, yabar koyarwa bayan an nadashi Shugaban Daraktoci na (NITDA) wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nadashi a watan Satumba 26, shekarar 2016.
Dr Pantami ya kasance malamin islama kuma mai jagorantar sallar Juma’ah sama da shekara 20 a Najeriya dama Kasar Ingila.
Ya kasance mamba a kwamitin amuntattu na Bankin Ja’iz, sannan kuma mamba ne na Shurah kuma mataimakin Babban Sakataren Kotun Shari’ah ta kololuwa (SCS) ta Najeriya.
A shekarar 2008, yayi mukabala da shugaban kungiyar Boko Haram, marigayi Muhammad Yusuf akan akidar Boko Haram data Salaf.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter:http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng