Farashin Pampers, Ariel, Oral B, Zai Tashi Yayin da Kamfanin P&G Ya Dakatar da Aiki a Najeriya

Farashin Pampers, Ariel, Oral B, Zai Tashi Yayin da Kamfanin P&G Ya Dakatar da Aiki a Najeriya

  • Kamfanin Amurka, mai sarrafa Pampers, Always, Oral B, Ariel, Ambi-pur, SafeGuard, Olay da Gillette ya sanar da daina aiki a Najeriya
  • Kamfanin mai suna P&G ya yanke shawarar rufe kamfaninsa ne sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasar
  • Sai dai kamfanin ya ce maimakon sarrafa kayakkin a cikin Najeriya, zai rinka shigo da su daga kasar waje don sayarwa ga 'yan kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

New York - Wani babban kamfanin Amurka mai sarrafa kayayyakin amfanin gida, Procter & Gamble, da aka fi sani da P&G ya sanar da rufe ma'aikatar sarrafa kayayyakinsa a Najeriya.

Babban jami'in kudi na kamfanin, Andre Schulten, ya sanar da hakan a wani taron kamfanoni da 'yan kasuwa na Morgan Stanley a New York, ranar Talata.

Kara karanta wannan

Da kamar wuya: Zai yi wahala Mmatatun Najeriya su yi aiki inji tsohon shugaban NNPC

Procter & Gamble ya dakatar da ayyukansa a Najeriya
P&G dai shi ke samar da kayyakin amfanin gida a Najeriya da suka hada da Pampers, Always, Oral B, Ariel, Ambi-pur, SafeGuard, Olay da Gillette. Hoto: Getty Images, ProcterGamble
Asali: Getty Images

P&G dai shi ke samar da kayyakin amfanin gida a Najeriya da suka hada da Pampers, Always, Oral B, Ariel, Ambi-pur, SafeGuard, Olay da Gillette, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya sa P&G zai dakatar da aiki a Najeriya?

A cewar Schulten, kamfanin P&G zai dawo shigo da kayansa zuwa Najeriya maimakon sarrafa su a cikin kasar, wanda hakan zai jawo akalla mutum 5,000 su rasa ayyukansu.

Ya kara da cewa hakan ya biyo bayan matsaloli na muhalli da kuma rashin darajar Naira akan Dala, wanda ya tilasta kamfanin daukar wannan mataki, rahoton The Cable.

Ya ce:

"Idan ka duba kasar Najeriya da Argentina, muna shan wahala wajen gudanar da ayyuka saboda rashin tattalin arziki mai kyau, da lalacewar kudin kasar akan dalar Amurka.
"Wannan garambawul ya shafi kasashen Najeriya da Argentina ne kawai. Mun sanar da cewa za mu rinka shigar da kayanmu Najeriya ne kawai, hakan na nufin rufe kamfanin sarrafa kayanmu."

Kara karanta wannan

Gwamna ya matsawa EFCC ta kama tsohon ministan Buhari kan wasu dalilai, bayanai sun fito

Sai dai ana ganin wannna matakin, zai tilasta karuwar farashin kayayyakin, la'akari da cewa yanzu shigowa da su kamfanin zai rinka yi, sabanin yadda yake sarrafa su cikin kasar a baya.

Jam'iyyun siyasa 7 a Najeriya sun hade kai

A wani labarin, jam'iyyun adawa bakwai ne suka hada kansu karkashin kungiyar hadakar jam'iyyu (CCPP) don kawo karshen mulkin APC a Najeriya.

Jam'iyyun sun hada da PDP, NNPP, ADC, APM, SDP da kuma ZLP, wadanda suka yi yakinin hadakar za ta bunkasa dimokuradiyya, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel