Yadda Cikin Shekara 24 Najeriya Ta Yi Abin Da Amurka Ta Kasa Yi Sai Bayan Shekara 185, Akpabio

Yadda Cikin Shekara 24 Najeriya Ta Yi Abin Da Amurka Ta Kasa Yi Sai Bayan Shekara 185, Akpabio

  • Sanata Akpabio ya ce Najeriya ta kafa wani tarihi da ya dauki kasar Amurka shekaru 185 duk da cewa shekarun Amurka 247 da fara dimokuradiyya
  • Shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da Tinubu ya gabatar da kasafin naira tiriliyan 27.5 gaban majalisar tarayya
  • Akpabio ya ce Najeriya ta samar da tsaffin 'yan majalisun dattawa matsayin shugaban kasa da mataimakinsa a cikin shekaru 24

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce a cikin shekaru 24 kacal, Najeriya ta samu nasarar da ta dauki Amurka tsawon shekaru 185.

Akpabio ya bayyana hakan ne a zaman hadin guiwa na majalisar wakilan tarayya da dattawa yayin da Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin naira tiriliyan 27.5 a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya isa majalisa domin gabatar da kasafin kudi, bayanai sun fito

Godswill Akpabio/Joy Bidden/Najeriya/Amurka
Godswill Akpabio, ya ce a cikin shekaru 24 kacal, Najeriya ta samu nasarar da ta dauki Amurka tsawon shekaru 185. Hoto: @SPNigeria/@POTUS
Asali: UGC

Tarin da Najeriya ta kafa da ya doke Amurka

Shugaban majalisar ya ce yayin da Najeriya ta samar da tsaffin sanatoci matsayin shugaban kasa da mataimaki a shekaru 24, ya dauki Amurka akalla shekaru 185, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A shekarar 1992 aka zabi Shugaba Tinubu a matsayin dan majalisar dattawa a jamhuriya ta uku da ba ta dade ba, yayin da Kashim Shettima ya zama sanata a shekarar 1999.

A Amurka, Shugaba John F Kennedy da mataimakinsa Lyndon B Johnson sun sami shiga fadar White House lokacin da dimokuradiyyar Amurka ke bikin cika shekaru 185 da kafuwa.

Bambanin shekarun dimokuraddiyar Najeriya da Amurka

Yayin da ya ke jinjina wa kokarin Tinubu na habbaka tattalin arziki, shugaban majalisar datta, ya ce:

"Mai girma shugaban kasa, kana sane da cewa dimokuradiyyar Amurka ta fara shekaru 247 baya. Amma sai da ta cika shekaru 185 sannan ta samu shugaba da mataimaki tsaffin 'yan majalisu.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa Sun Hadu, An Huro Wuta a Janye Takunkumi, a Maidawa Nijar Kasar Wuta

"Amma mu a Najeriya, shekaru 24 kawai hakan ya dauke mu, muka samar da shugaba da mataimaki tsaffin 'yan majalisaru, tarihin da ya dauki Amurka shekaru 185."

Akpabio ya ce ban da Tinubu da Shettima da suka taba zama 'yan majalisar dattawa, akwai wasu tsaffin 'yan majalisar da ke rike da mukamai a gwamnatin Najeriya.

Kotun koli ta yanke hukunci kan amfani da tsaffin naira

A wani labarin, kotun Kolin Najeriya ta yanke hukunci kan bukatar da gwamnatin Tinubu ta gabatar mata na kara wa'adin amfani da tsaffin takardun naira, Legit Hausa ta ruwaito.

A hukuncin da kotun ta yanke a ranar Laraba, ta ce yanzu 'yan Najeriya za su iya ci gaba da amfani da tsaffi tare da sabbin kudin har illa-ma-shaa-Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel