Kus-kus: Ganduje Ya Shiga Ganawar Sirri da Gwamna Mai Mala Buni, Ubah da Wasu Jiga-Jigan APC

Kus-kus: Ganduje Ya Shiga Ganawar Sirri da Gwamna Mai Mala Buni, Ubah da Wasu Jiga-Jigan APC

  • Jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) ta shiga wata ganawar sirri da wasu gwamnoni da jiga-jigan jam'iyyar a Abuja
  • Kadan daga cikin mahalarta taron sun hada da gwamnan jihar Imo, Nasarawa, Yobe da mataimakin shugaban majalisar dattawa
  • Duk da cewa ba a bayyana dalilin taron ba, sai dai wata majiya daga sakatariyar jam'iyyar ta bayyana cewa taron zai mayar da hankali kan jihar Anambra

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Rahotannin da muke samu na nuni da cewa Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma da takwaransa na jihar Nasarawa, Abdullahi Sule sun saka labule da Abdullahi Ganduje a Abuja.

Sauran mahalarta taron sun hada da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni; mataimakin shugaban majalisar dattawa, Jibrin Barau, da kuma wasu tsaffin 'yan takarar gwamnan Anambra, Sanata Ifeanyi Ubah da Uche Ekwunife.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno PDP yayin da Atiku da fitaccen gwamna suke neman iko, karin bayani

Abdullahi Ganduje/Jam'iyyar APC
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya shiga ganawa da wasu gwamnoni da jiga-jigan jam'iyyar a Abuja. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Jiga-jigan jam'iyyar ta APC sun isa harabar sakatariyar jam'iyyar da misalin karfe 12:30 na rana a ranar Laraba inda suka samu kyakkyawar tarba daga Abdullahi Ganduje, shugaban jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ganawar ta kunsa?

Haka zalika an ruwaito cewa tsohon sanatan Anambra ta Kudu kuma jigon jam'iyyar, Andy Uba na daga cikin wadanda suka halarci zaman, The Punch ta ruwaito.

Duk da cewa ba a bayyana dalilin wannan ganawar ba, sai dai wata majiya daga sakatariyar ta ruwaito cewa jam'iyyar na kokarin yin garambawul a jam'iyyar reshen jihar Anambra.

Yin hakan a cewar majiyar zai taimaka wa jam'iyyar wajen kara mata karbi a zaben gwamnan jihar, shugaban kasa da kuma na 'yan majalisun jihohi da na tarayya.

Manyan Arewa: Tinubu bai damu da matsalar tsaro ba

A wani labarin, kungiyar dattawan Arewa ta caccaki shugaban kasa Bola Tinubu kan mayar da hankali a lamuran tattalin arziki maimakon tsaro a kasar.

Kara karanta wannan

APC ta samu karuwa bayan manyan sanatoci guda 2 sun watsar da jam'iyyarsu da magoya bayansu

Farfesa Usman Yusuf, jigo a kungiyar NEF, ya ce ya zama wajibi Shugaba Tinubu ya kafa kwamiti don bincike kan harin da aka kai jihar Kaduna, Legit Hausa ta ruwaito.

Kungiyar ta kuma gargadi shugaban kasar da ya tsame hannun jami'an soji daga wannan bincike, ya bar hukumomin fararen hula su yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel