Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari makarantar Soji NDA, sun hallaka Soja 2, sun sace 1

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari makarantar Soji NDA, sun hallaka Soja 2, sun sace 1

Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa wasu tsagerun yan bindiga sun kai mumunan hari makarantar horar da Sojin Najeriya NDA dake jihar Kaduna.

Rahoton ya nuna cewa yan bindigan sun hallaka mutum biyu yayinda suka yi awon gaba da jami'in Soja guda daya.

A riwayar Daily Trust kuwa, jami'in Sojan ruwa ne aka kashe yayinda mutum biyu da aka sace masu matsayin Manjo ne.

An tattaro cewa yan bindigan sun kai farmakin ne misalin karfe 1 na dare kuma da alamun har yanzu suna ciki.

Wata majiya da ta bukaci a sakaye sunanta ta bayyanawa DailyTrust cewa yanzu dai an dinke barikin dommin hana yan bindigan samun daman guduwa da Sojan da suka dauke.

Yace:

"Ai abin takaici ne matuka, yan bindigan sun kawo farmaki ne lokacin da mutanen bariki ke bacci."

Kara karanta wannan

Mahaifiyar SSG na jihar Bayelsa da aka sace ta kubuta daga hannun 'yan bindiga

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yanzu haka an kulle barikin gaba daya saboda hana yan bindigan fita don ana tunanin har yanzu suna ciki."

Daya daga cikin Sojojin da aka jikkata yanzu haka yana asibiti yana jinya.

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari makarantar Soji NDA, sun sace Soja 1
Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari makarantar Soji NDA, sun sace Soja 1
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel