Nigerian news All categories All tags
Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo sun yi ido-biyu da Atiku Abubakar

Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo sun yi ido-biyu da Atiku Abubakar

Dazu mu ka samu labari cewa an yi ido-biyu tsakanin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar da tsohon Mai gidan sa Cif Olusegun Obasanjo a wajen wani taro a Abuja.

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya hadu da Wazirin Adamawa Atiku Abubakar jiya a babban otel din nan na Transcorp Hilton da ke Birnin Tarayya Abuja inda aka yi wani taro domin gyara alakar Najeriya da Kasar Sin.

Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo sun yi ido-biyu da Atiku Abubakar

Obasanjo da Atiku Abubakar sun gana a Abuja jiya

Ba a dai saba ganin Cif Olusegun Obasanjo da Atiku Abubakar ba tun bayan da su ka samu sabani a baya. Janar Aliyu Gusau wanda tsohon mai bada shawara kan harkar tsaro na Kasar ne ya hada manyan ‘Yan siyasan a wajen taron.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP na zaman makokin kashe-kashen Filato

An dai ga Tsohon Shugaban Kasar da kuma Mataimakin na sa su na gaisawa kamar ba su taba samun sabani ba. Ko a kwanan nan ma Atiku ya caccaki tsohon Shugaban Kasar game da kudin da aka kashe kan wutan lantarki a Najeriya.

Laftanan Janar Aliyu Gusau ya rikewa Olusegun Obasanjo ofishin NSA har zuwa lokacin da ya bar mulki a 2007. Bayan hawan Goodluck Jonathan mulki a 2010 ne Aliyu Gusau ya dawo ofishin sa na bada shawara kan harkar tsaro a Najeriya.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa tsohon hugaban Kasar Benin watau Boni Yayi da kuma tsohon Shugaban Kasar Nijar Mahamane Ousmane sun halarci wannan babban taro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel