Fankon Kundin Kasafin Kudi Tinubu Ya Gabatarwa Yan Majalisa? Daga Karshe Gaskiya Ta Bayyana

Fankon Kundin Kasafin Kudi Tinubu Ya Gabatarwa Yan Majalisa? Daga Karshe Gaskiya Ta Bayyana

  • Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada a Kano, Alhassan Doguwa ya yi karin haske kan kasafin kudin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar na 2024
  • Doguwa ya karyata ikirarin Yusuf Galambi na cewa fankon kundin shugaban kasar ya gabatarwa yan majalisun tarayya
  • Sabanin haka, dan majalisar na APC ya ce Tinubu ya gabatar da na'ura mai dauke da kunshin kasafin kudin kafin jawabinsa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Doguwa/Tudun Wada a Kano, Alhassan Doguwa, ya yi watsi da ikirarin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatarwa yan majalisa da fankon kasafin kudin shekara mai zuwa.

A hirar da aka yi da shi a sashin Hausa na BBC, wani mamba na jam'iyyar adawa ta NNPP, Yusuf Galambi, ya yi zargin cewa babu abin da su ka samu a cikin kwalayen da shugaba Tinubu ya gabatarwa majalisar tarayyar.

Kara karanta wannan

"Akwai kotun Allah": Martanin jama'a bayan kotu ta yanke hukunci a shari'ar Abba da Ado Doguwa

Doguwa ya ce ba fankon kwalin kasafin kudi Tinubu ya gabatarwa majalisa ba
Tinubu Ya Mika Na'ura Dauke da Kunshin Kasafin 2024, Ado Doguwa Ya Caccaki Abokin Aikinsa Hoto: Alhassan Doguwa, Bola Ahmed Tinubu, Yusuf Galambi
Asali: Twitter

Galambi, dan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram a Jigawa ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun duba kundin takardar da ya gabatar sai muka ga babu komai a ciki. A tarihin majalisar dokokin tarayya, irin haka bai taba faruwa ba sai a shekarar nan kuma wannan ba shine abun da kundin tsarin mulkin kasar ya ce ayi ba."

Doguwa ya ce Tinubu ya gabatarwa yan majalisa da kwafin kasafin kudin 2024 a na’ura

Amma da yake jawabi ga manema labarai a ranar Juma'a, 1 ga watan Disamba, Doguwa ya dage cewa yan majalisa sun samu cikakken kunshin kasafin kudin Tinubu kafin jawabin da ya yi a gaban majalisun biyu, rahoton Punch.

Doguwa ya ce:

"Abun da mutane basu sani ba shine cewa tuni Shugaban kasa Tinubu ya gabatar da na'ura na gaba daya kunshin kasafin kudin kafin jawabinsa a gaban majalisar hadin gwiwar."

Kara karanta wannan

Babu Komai a kwalayen kasafin kudin da Shugaba Tinubu ya kawo – ‘Dan Majalisar NNPP

Ya bayyana ikirarin cewa fankon kwalin kasafin kudi yn majalisar suka samu a matsayin mara tushe balle makama, rahoton The Cable.

Doguwa ya fayyace cewa kamar yadda aka saba, Tinubu ya ba da kwafin jawabinsa tare da na'urar da ke dauke da kwafin cikakken kasafin kudin da yadda za a kashe su.

Dan majalisar ya bukaci a daina juya gaskiya da gangan dangane da gabatar da kasafin kudin da fadar shugaban kasa tayi.

“A daina juya gaskiya, ba mu karbi fankon kwalin kasafin kudin 2024 ba daga hannun Shugaba Tinubu ba,” in ji shi.

An bukaci Tinubu ya inganta tattalin arziki

A wani labari na daban, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa Primate Elijah Ayodele ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu da ta inganta tattalin arziki a kasar.

Ayodele ya yi hasashen cewa idan har aka gaza yin haka, za a yi gagarumar zanga-zanga kan gwamnatin APC a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel