Dan Najeriya Ya Raba Daloli a Unguwa, Kirkinsa Ya Tsorata Mata, Sun Tsere a Bidiyo

Dan Najeriya Ya Raba Daloli a Unguwa, Kirkinsa Ya Tsorata Mata, Sun Tsere a Bidiyo

  • Wani dan Najeriya ya shiga unguwa sannan ya dunga rabawa mutanen da bai sani ba daloli ba tare da ya furta komai ba
  • Wasu mata biyu da yar budurwa sun ji tsoron taba kudin ma yayin da suke tunanin kodai wani asiri ne
  • Yan Najeriya da dama da suka ga bidiyon sun bayyana cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen karbar kudin idan har suka samu damar yin haka

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani dan Najeriya wanda kan shirya bidiyoyin zolaya ya yi aikin alkhairi yayin da ya yi wa mutanen da bai sani ba kyautar kudi a unguwa.

Mutumin (@teaserprank_) ya shiga unguwa da daloli sannan yana ta mika su ga mutane, yana mai ce masu su karba su ji dadinsu.

Kara karanta wannan

"Cin zabe sai an hada da rauhanai" Shehu Sani ya yi wa Doguwa martani

Matashi ya raba daloli a unguwa
Dan Najeriya Yana Raba Daloli a Unguwa, Kirkinsa Ya Tsorata Mata, Sun Tsere a Bidiyo Hoto: @teaserprank
Asali: TikTok

Rabon daloli a unguwar Najeriya

Daga cikin mutane da dama da ya tunkara, matashiya daya ce kawai ta yi karfin halin karbar dalolin ba tare da ta yi mugun tunani a kai ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata mata ta yi tunanin mutumin zai yi asirin ne da ita da wannan kudin. Ta fatattake shi harda amfani da katako.

Yan Najeriya da dama sun yi mamakin dalilin da yasa tsoffin matan suke jin tsoron karbar dalolin a bidiyo.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani ga bidiyon kyautar daloli

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

Majesty the photographer ya ce:

"Tsoffin matan sun kai mizanin da za su fahimci cewa a wannan duniyar babu wani abu da yake na kyauta."

sydney musenge ya ce:

"Lallai talauci ya sauya yanayin tunaninmu."

alukoayodeji ya ce:

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda malami ya jagoranci dalibansa wajen ciccibo yaron da ke yawan fashin makaranta ya yadu

"Na rantse yanayin tunaninmu ma wani matsala ne na karan kansa."

shuga ta ce:

"Duk sun yi tunanin kudin asiri ne."

Tejiri:

"Idan ban karba ba na tafi a tsaye."

Abigail:

"Ba za ku ga laifinsu ba..saboda mutane na amfani da dala wajen yin asiri a zahirin gaskiya."

Uwargidar Tinubu ta rabawa mata kudi

A wani labari na daban, mun ji cewa mutum akalla 1, 709 za su amfana da gudumuwar N250, 000 da uwargidar shugaban kasar Najeriya, Oluremi Tinubu ta raba.

Rahoton This Day ya ce matar shugaba Bola Tinubu ta yi wannan dawainiya karkashin gidauniyarta, Renewed Hope Initiative (RHI).

Asali: Legit.ng

Online view pixel