An Cire Wasu Mutane Yayin Da CBN Zai Fara Rabon Kudi Ga Talakawa Miliyan 5

An Cire Wasu Mutane Yayin Da CBN Zai Fara Rabon Kudi Ga Talakawa Miliyan 5

  • Gwamnatin tarayya ta na shirin karkare yadda za a aikawa iyalai kudi domin rage radadin talauci da miliyoyin mutane su ka shiga
  • Gidaje miliyan biyar ake sa ran za su samu N25, 000 a watannin Oktoba, Nuwamba da Disamba a karkashin tsarin nan na CCT
  • Daga makon da za a shiga, mutane za su rika jin kudi sun shigo asusunsu, daga cikin sharadin dole sai an mallaki lambobin BVN da NIN

Abuja - Gwamnati ta na duba yadda za ta kara adadin mutanen da za su amfana da tsarin rabon kudi domin rage radadin talauci a Najeriya.

Wani dogon rahoton Punch ya ce ana so a cusa sunayen ‘yan fansho da wasu tsofaffin sojoji a jerin wadanda za a rika rabawa kudi a wata.

Haka kuma ana cire sunayen wadanda su ka rasu domin tsabtace rajistar biyan kudin.

Kara karanta wannan

Uwar Bari: An Bada Shawarar Amfani da Man-Ja a Jiragen Sama Saboda Tsada

Shugaba Tinubu
Bola Tinubu zai rabawa talakawa N25, 000 Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Sai da BVN & NIN za a biya kudi

Duk wani wanda bai da lambar NIN ta shaidar zama ‘dan kasa da lambar BVN ta banki ba zai samu kudin da bankin CBN zai fara rabawa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kai-tsaye babban bankin zai rika raba kudin daga makon gobe, ba ta hannun wasu ba.

Hikimar amfani da NIN da BVN shi ne a bankado sunayen bogi da aka cusa, kuma a tabbatar da cewa kudin zai je ga wadanda aka nufa.

Minista ta fadi yadda za a raba N25, 000

Mai taimakawa Ministar jin kai da yaki da talauci wajen hulda da jama’a da yada labarai, Rasheed Olanrewaju ya yi karin haske a kan tsarin.

Olanrewaju ya tabbatar da cewa za su yi amfani da rajistar da Muhammadu Buhari ya yi aiki da ita, sannan za a kara wasu sunayen dabam.

Kara karanta wannan

Za Su Kashe Ni – Abokin Fadan Kwankwaso a NNPP Ya Ce Ya Na Fuskantar Barazana

Hadimin Ministan ya ce daga makon gobe za a fara fitar da tulin kudi domin a biya kudin, ya ce har an soma biyan wadanda aka tantance.

Shugaban sashen sadarwa na tsarin NSIPA, Jamaldeen Kabir ya tabbatar da cewa an cire sunayen wadanda su ka fita daga sahun talakawa.

NSIPA za ta taimakawa marasa karfi

A baya an ji labari cewa shugabar NSIPA, Halima Shehu ta fadawa Majalisa cewa hukumarta za ta raba N5000 da jarin N150, 000 ga mutane.

Cire tallafin man fetur ya jawo karin tsadar rayuwa a Najeriya, saboda haka Gwamnatin tarayya ta ci bashin $800m daga bankin Duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel