Bidiyon Yadda Malami Ya Jagoranci Dalibansa Wajen Ciccibo Yaron da ke Yawan Fashin Makaranta Ya Yadu

Bidiyon Yadda Malami Ya Jagoranci Dalibansa Wajen Ciccibo Yaron da ke Yawan Fashin Makaranta Ya Yadu

  • Malami ya yi wa wani dalibinsa da ke da dabi'ar fashin zuwa makaranta wani abu da bai taba zataba
  • Malamin mai kishi ya tara dalibansa domin su je gidan yaron sannan su dauko shi zuwa makaranta a kan kafadunsu
  • Wani bidiyo da ke nuna yadda suka dauko yaron uwa harabar makaranta ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abokan karatun wani yaro da ke yawan fashin zuwa makaranta sun ciccibo shi zuwa makaranta bayan malaminsa ya shirya hakan.

Wan dan gajeren bidiyo da Angel FM Kumasi 96.1 ya wallafa a Facebook ya nuno lokacin da aka dauko yaron zuwa makaranta.

Dalibai sun ciccibo yaron da baya son zuwa makaranta
Bidiyon Yadda Malami Ya Jagoranci Dalibansa Wajen Dauko Yaron da ke Yawan Fashin Makaranta Ya Yadu Hoto: Angel FM Kumasi 96.1
Asali: Facebook

A cikin bidiyon, malamin ya jagorance su rike da bulala a hannunsa. Dalibansa sun take masa baya dauke da abokin karatun nasu mara jin magana a kafadunsu.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda wani matashi ya tarwatsa bikin auren tsohuwar budurwarsa ya girgiza intanet

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wani malami ya jagoranci dalibansa don kamo wani dalibi da ke yawan fashin zuwa makaranta," taken da aka rubuta jikin bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani ga abun da malamain ya aikata

Godwin O Asare ya ce:

"Yaron zai canja sannan ya mayar da martani ga wannan rana dauke da murmushi."

Reginald Abbey ya ce:

"Yawancin yaran da suke kin zuwa makaranta suna yin hakan ne saboda ba sa jin dadin darussa, koyarwa da kuma wulakanci daga wasu dalibai da malamai.
"Saboda haka ya kamata malami ya samo hanyoyi masu ban sha'awa da sababbin dabaru don koya masa da kuma sanya shi jin dadi a cikin aji..."

Abanga Moses ya ce:

"Suna yi mana wannan abun a baya.
"Har yanzu ina tuna yadda na kubuta daga wannan lamarin ta hanyar shawo kan iyayena don su fada musu cewa ba ni da lafiya bayan na ga sun zo kusa da gidana. Yayin da yayana ya yi tsalle a cikin haramtacciyar hanya (wadanda suka fito daga gabas za su fahimta), Hankali kwance na shirya dabara da ya yi mun aiki da kyau.

Kara karanta wannan

Bidiyon zanga-zangar da ta barke a Kano kan zargin 'yan sanda sun kashe farar hula

"Yau ni malami ne Allah ya sakawa malamai masu kokari."

Iddris Tk ya ce:

"Muna son wannan hali daga malamai. Zamanin ya wuce . Muna son shi . Ku dawo da shi."

An tarar iyali na cin abinci bayan rasa mahaifi

A wani labari na daban, mun ji cewa wani rubutu da ya yi fice a Twitter, wani dan Najeriya ya tuna wani abun ban mamaki da ya gani wani lokaci da ya gabata.

Mutumin mai suna @FotoNugget a Twitter ya ba da labarin yadda abokan arziki suka ziyarci wasu iyali da sassafe bayan mahaifinsu ya rasu cikin dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng