Tsohon Gwamnan da Ake Zargi Ya Sace N70bn Ya Rabawa Mutane Goron Sallar N200m

Tsohon Gwamnan da Ake Zargi Ya Sace N70bn Ya Rabawa Mutane Goron Sallar N200m

  • Bello Muhammad Matawalle ya jika hantar magoya baya, marayu da malaman addini a Zamfara
  • Tsohon Gwamnan na Zamfara ya raba N200m yayin da Musulmai ke shirye-shiryen babbar sallah
  • Abin mamaki, kwanan nan Matawalle ya sauka daga kujerar Gwamna bai biya ma’aikata albashi

Zamfara - Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, wanda a yanzu ana tuhumarsa da taba dukiyar al’umma, ya yi rabon miliyoyi domin shirin babbar sallah.

A makon nan ne za ayi bikin sallah a fadin Duniya, Premium Times ta ce Bello Muhammad Matawalle ya rabawa ‘yan jam’iyyarsa Naira miliyan 200.

Shugaban APC a Zamfara, Tukur Danfulani ya tabbatar da haka a wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce ‘yan jam’iyya sun samu kudin hidimar sallah.

Tsohon Gwamna
Bello Matawalle a lokacin ya na Gwamna Hoto: Getty Images/Anadolu Agency
Asali: Getty Images

An fara rabawa mutane kudi

Danfulani ya nuna masu ruwa da tsaki, mata, matasa, sauran magoya baya da kuma marayu, malaman addini, da masu tallata APC za su amfana da kudin.

Kara karanta wannan

Babban Sallah: Sanata AbdulAziz Yari Ya Yi Wa Wasu Zamfarawa Tagomashin Alkhairi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamiti na musamman ya fara aiki domin a rabawa al’umma kudin. Shugaban jam’iyyar ya ce an yi hakan ne domin mutane su ji dadin bikin sallah.

Rahoton ya kara da cewa shugaban jam’iyyar na reshen jihar Zamfara, ya godewa tsohon Gwamnan, ya ce kyautar ta zo a lokacin da aka fi bukatarta.

EFCC ta na bincike a kan Matawalle

Sai dai inda gizo ke sakar, kafin Alhaji Matawalle ya bar ofis, rahotanni sun zo cewa hukumar EFCC ta na zarginsa da karkakatar da N70bn daga baitul-mali.

Darektan hulda da jama’a na hukumar, Osita Nwajah ya ce gwamnatin Zamfara ta rika bada kwangilolin bogi, har aka yi nasarar wawurar biliyoyin kudi.

Ba a nan abin ya tsaya ba, ma’aikatan jihar Zamfara sun yi watanni ba tare da albashi ba a karshen mulkin Matawalle, rabon wasu da albashi tun a Fabrairu.

Kara karanta wannan

Tserewa Zai Yi: Gwamnati Ta Haskawa Kotu Hadarin Bada Belin Godwin Emefiele

Babu dalilin da aka bada a lokacin na rashin albashin, sai ga shi ana yabon tsohon Gwamnan saboda rabon miliyoyi ga magoya bayan da marasa karfi.

Haka aka ji Abdulaziz Yari ya rabawa mutanensa raguna 500 domin layya. Yari wanda yanzu Sanata ne ya yi gwamna, shi ma EFCC ta na bincikensa.

Ana neman Matawalle a yanzu?

Kwanaki sai da rade-radi ya fara yawo cewa Hukumar EFCC ta na farautar tsohon Gwamna, Bello Muhammad Matawalle saboda zargin ya tafka sara.

Tun kafin tsohon Gwamnan na Zamfara ya fito ya ce uffan, sai aka ji Kakakin EFCC ya na karyata rahoton, ya kuma ce ba su ba DSS damar cafke shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel