Yan Bindiga Sun Sace Malamin Addinin Musulunci da Amarya da Ango a Kaduna
- Yan bindiha sun farmaki mazauna yankin Dan-Honu da ke Millennium City, karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna
- Maharan sun yi garkuwa da malamin addinin musulunci da iyalinsa da kuma sabbin ma'aurata
- Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta fatattaki maharan tare da kubutar da wadanda aka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Wasu yan bindiga sun farmaki al'ummar Dan-Honu da ke Millennium City, karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka sace sabbin ma'aurata, malamin addinin musulunci da wasu mutane a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba.
An tattaro cewa maharan sun kai hari ne sanye da bakaken kaya da bindigogin AK47 su da yawa da misalin karfe 9:00 na dare.
Wani majiya wanda ke zaune a yankin ya fada ma jaridar Punch cewa yan bindigar sun yi awon gaba da akalla mutum takwas a yankin ciki harda ma'aurata, limami da sauran jama'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma, majiyan ya kara da cewar limamin da wani mutum daya sun tsere yayin da ake kora su zuwa cikin jeji.
Ya ce:
"Yan bindigar da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun zo a daren ranar Talata, suka farmaki al'ummar Dan-Honu II a New Millennium City, karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sannan suka yi garkuwa da mutane takwas.
"Daga cikin wadanda aka sace akwai sabbin ma'aurata da suka yi aure a ranar Asabar da ta wuce, limamin masallacin garin, matarsa da yaransu uku, ciki harda yaro dan wata 10.
"Yan bindigar sun farmaki garin da misalin 8:50 na dare kimanin su 10, tare da bindigogin AK47 da sauran makamai, cikin bakakken kaya, sannan dayansu na sanye da takunkumin fuska.
"Mun tsallake rijiya da baya. Yan bindihar sun fara da daukar limamin da iyalinsa wadanda suka tarar a wajen masallacin Juma'ar garin kafin suka isa ga sauran gidaje inda suka sace sabbin ma'auratan.
"Ina cikin dakina lokacin da yan bindigar suka farmaki harabar gidanmu. Da farko, da suka fara buga kofar sabbin ma'auratan, na zata jami'an tsaro ne suka zo kama makwabtana saboda kai tsaye suka nufi dakinsu."
Ya ci gaba da cewa:
"Sun fara bubbuga kofarsa da ihun ‘Dan Iska ba za ka fito ba?’, lokacin ne na gane cewa masu garkuwa da mutane ne. Saboda haka, da suka kasa bude kofar, sai suka fasa taga sannan suka balle karfen tagar.
"Da suka samu shiga dakin, yan bindigar sun yi kokarin bude kofar, amma sun gaza, don haka suka fito da ma'auratan ta fasasshiyar tagar. Sun raunata mijin kuma jini na ta zuba a jikinsa."
Malamin da aka sace ya magantu
Da yake bayanin halin da ya shiga, malamin wanda ya tsere daga hannun yan bindigar, ya fada ma manema labarai cewa biyu daga cikin yan bindigar da suka farmaki yankin na dauke da bindigogin AK47 da harsasai, yayin da sauran ke rike da adduna rahoton Nigerian Tribune.
Ya ce:
"Sun daki yaron dan wata 10 saboda yana kuka. Sun ma yi barazanar kashe shi saboda kukan shi na damunsu. Amma na gode Allah madaukakin sarki matata da yaron sun tsere bayan na tsere amma yan bindigar sun tafi da yarana maza biyu."
Rundunar yan sanda ta yi martani
Yayin da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya bayyana cewa jami'an sun fatattaki yan bindigar sannan sun ceto mutanen.
"Abun da muka sani shine cewa sun shiga, yan sanda sun fatattaki maharan sannan sun ceto wadanda aka sace."
Barayi sun kashe daraktan kudi a Ogun
A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu da ake zaton masu fashi da makami ne sun bindige Taiwo Oyekanmi, wani daraktan kudi kuma akanta da ke aiki a ofishin Gwamna Dapo Abiodun a Oke-Mosan, Abeokuta.
An bindige Oyekanmi ne a saman gadar NNPC yayin da yake dawowa daga banki inda ya je cire kudi a shirye-shiryen gabatar da kasafin kudi da gwamnan Ogun zai yi a ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba.
Asali: Legit.ng