Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Jihohin Arewa 2, Sun Sace Mutum 100 Saboda Dalili 1

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Jihohin Arewa 2, Sun Sace Mutum 100 Saboda Dalili 1

  • Tsagerun yan bindiga sun farmaki al'umma a jihohin Zamfara da Katsina a yankin Arewa maso Yammacin kasar
  • Maharan sun yi awon gaba da mutane kimanin 100 saboda rashin biyan wasu kudade da suka kakaba masu
  • A Zamfara, yan bindigar sun nemi mutanen garin Kwana su biya haraji naira miliyan 30, mutanen Sabon Garin Mahuta naira miliyan 20, yan Unguwar Kawo kuma naira miliyan 10

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Yan bindiga sun yi garkuwa da akalla mutum 100 bayan sun farmaki wasu kauyuka a jihar Katsina da karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Peoples Gazatter ta rahoto cewa wani dan kungiyar yan banga a Katsina ya sanar da ita cewa yan bindigar dauke da muggan makamai sun armaki mutanen yankin ne sanye da kayan sojoji.

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram sun datse kawunnan mutane 11 masu sana’ar itace a Borno

Mahara sun sace mutum 100 a Zamfara da Katsina
Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Jihohin Arewa 2, Sun Sace Mutum 100 Saboda Dalili 1 Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

An kuma tattaro cewa maharan sun farmaki garuruwan Zamfara ne a daren Juma'a bayan sallar Isha'i, rahoton PM News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna garuruwan Zamfara da yan bindigar suka kai hari da suka hada da Mutunji, Unguware Kawo, Kwantar Dutsi da Sabon Garin Muhata a yammacin ranar Juma'a, sun magantu.

A cewarsu, maharan sun zo ne a kan babura sannan suka yi gaba da mutane saboda garuruwan basu biya harajin da suka nema ba.

Gogarman dan bindiga Damina ya kakabawa al'ummar Zamfara biyan haraji

Sun bayyana sunan shugaban yan bindigar a matsayin "Damina", cewa shine ke jan ragamar yankin, musamman da rashin jami'an tsaro a jihar.

Yan bindigar sun farmaki Mutunji bayan mutanen kauyen sun gaza biyan naira miliyan 50 da Damina ya nema.

Daya daga cikin mutanen da aka sace a kauyen Mutunji wanda ya tsere daga hannun maharan, ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Abdul Amart da Rarara sun yi wa iyalan marigayi Aminu S Bono sha tara ta arziki

"Muna kokarin karbar kudaden... amma kwatsam sai yan bindigar suka zo suka yi wa mutane fashi. Sun yi awon gaba da mutum fiye da 100 - yawancinsu mata da matasa.
"Ya kuma sanya irin wannan haraji a sauran garuruwa. An nemi mazauna yankin Kwana da su biya naira miliyan 30, an nemi mutanen Sabon Garin Mahuta su hado naira miliyan 20, yayin da aka nemi yan Unguwar Kawo su hado naira miliyan 10.

Wani mazaunin kauyen ya nuna gajiyawarsa, ya ce:

"Yan ta'addan sune ke iko a yankin - suna tura mu daji don yi masu noma, sannan idan muka dawo, sai su shigo cikin garin don cin nama, shan shayi da kayan kwalba ba tare da sun biya ba."

Martanin yan sanda kan harin

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya ce ba zai iya yin karin bayani kan lamarin ba domin ya afku ne a yankin da sojoji suke.

Kara karanta wannan

Tsige Abba Gida Gida: An kama mutum 7 kan hukuncin Kotun Daukaka Kara, cikakken bayani

A bangaren Katsina kuma, ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ba.

Yan bindiga sun budewa yan sanda wuta

A wani labarin, mun ji cewa miyagun yan bindiga sun halaka ƴan sanda biyu da wani mutum ɗaya yayin da suka kai hari shingen binciken ababen hawa a jihar Imo.

Rundunar ƴan sanda reshen jihar Imo ce ta bayyana haka ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba, 2023, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng