Jimami Yayin da 'Yan Bindiga Su Ka Kai Mummunan Hari Sakatariyar Jiha Inda Su Ka Hallaka Akanta

Jimami Yayin da 'Yan Bindiga Su Ka Kai Mummunan Hari Sakatariyar Jiha Inda Su Ka Hallaka Akanta

  • 'Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Kuros Ribas inda su ka bindige wani akanta a ma'aikatar ilimi ta jihar
  • Maharan sun bi akantan ne har kusa da tsohon gidan gwamnati bayan sun biyo shi daga banki inda su ka kwace kudaden hannunshi
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, SP Irene Ugbo ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Larabar 29 ga watan Nuwamba a Calabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kuros Riba - Wasu 'yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Kuros Riba inda su ka yi ajalin wani akanta.

Akantan da ke aiki a ma'aikatar ilimi ta jihar ya rasa ransa ne a yau Laraba 29 ga watan Nuwamba, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Murna yayin da a karshe FG ta bayyana ranar biyan basukan masu cin gajiyar N-Power, ta fadi dalilai

Mahara sun bindige akantan jihar Kuros Riba tare da kwashe masa kudade
Yan bindiga sun hallaka akanta a jihar Kuros Riba. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Yaushe maharan su ka hallaka akantan?

Maharan sun bi akantan har zuwa kusa da tsohon gidan gwamnatin jihar kafin su ka harbe shi a cinya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Nigerian ta tattaba cewa maharan sun biyo akantan tun daga banki inda ya je cire kudade har zuwa inda su ka yi ajalinshi.

Birinin Calabar a kwanakin nan na fama da hare-haren 'yan bindiga musamman a kan babura.

Mene 'yan sanda su ka ce kan harin?

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan su guda biyu sun tilasta akantan ba su jakar kudin kafin bindige shi har lahira.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, SP Irene Ugbo ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Larabar 29 ga watan Nuwamba a Calabar.

Irene ya ce an kwashi akantan zuwa asibitin sojojin ruwa don ba shi kulawar gaggawa.

Kara karanta wannan

An bankado sabon shirin tayar da hargitsi a jihar Kano kan hukuncin tsige Gwamna Abba

Ya kuma yi Allah wadai da harin inda ya ce jami'ansu sun bazama don zakulo wadannan mahara.

Soja ya mutu a hatsarin jirgin ruwa

A wani labarin, wani jami'in soja ya rasa ransa yayin wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a jihar Ribas.

Lamarin ya faru ne a karshen makon nan a cikin kogi yayin da igiyar ruwa ta yi jifa tare da kifar da jirgin ruwa.

Rundunar sojin ta shiyya ta 6 sun yi martani inda su ka nuna alhinin rasuwar sojan da su ka bayyana ya na da kishin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel