Yan Bindiga Sun Kashe Akantan Gwamnati a Wata Jiha, Sun Sace Miliyoyin Naira, Cikakken Bayani

Yan Bindiga Sun Kashe Akantan Gwamnati a Wata Jiha, Sun Sace Miliyoyin Naira, Cikakken Bayani

  • Yan fashi da makami sun kashe Taiwo Oyekanmi, wani akanta da ke aiki tare da gwamnatin jihar Ogun
  • Makasan sun kuma sace kudi na miliyoyin naira da ake tunanin mallakin gwamnati ne
  • Legit Hausa ta samu labarin cewa yan fashin biyar sun kai wa Oyekanmi harin kautan bauna bayan ya karbo kudi daga banki a Abeokuta a hanyarsa ta komawa ofis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abeokuta, jihar Ogun - Wasu da ake zaton masu fashi da makami ne sun bindige Taiwo Oyekanmi, wani daraktan kudi kuma akanta da ke aiki a ofishin Gwamna Dapo Abiodun a Oke-Mosan, Abeokuta.

An bindige Oyekanmi ne a saman gadar NNPC yayin da yake dawowa daga banki inda ya je cire kudi a shirye-shiryen gabatar da kasafin kudi da gwamnan Ogun zai yi a ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Yanzu: Tashin hankali yayin da jami'an NSCDC suka harbi dalibai a Abuja yayin jarrabawa

Barayi sun kashe Akantan gwamnati
Yan Bindiga Sun Kashe Akantan Gwamnati a Wata Jiha, Sun Sace Miliyoyin Naira, Cikakken Bayani Hoto: Taiwo Oyekanmi, Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Barayi sun kashe daraktan kudi a Ogun

Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, barayin sun tare motar kudin da marigayin ke ciki a gadar Kuto, inda suka harbi Oyekanmu, suka fasa kofar motar da guduma, sannan suka yi awon gaba da kudin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, an kwashi Oyekanmi da sauran hadiman da suka ji rauni sakamakon harbi a yayin hare-haren zuwa babban asibitin jihar da ke Ijaye, inda akantan ya rasu daga baya.

Legit Hausa ta samu labarin cewa daraktan kudin da ya mutu ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa kwanaki hudu da suka wuce, a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba.

Yan sanda sun rufe hanyoyin fita daga Ogun

A halin da ake ciki, Abiodun Alamatu, kwamishinan yan sandan jihar, ya tabbatar da lamarin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan hari jihohin arewa 2, sun sace mutum 100 saboda dalili 1

Shugaban yan sandan ya bayyana cewa jami'ansa na yin iya bakin kokarinsu don kama barayin.

"Na umurci kwamandan yankin da ya je bankin sannan ya bukaci a ba shi kamarar CCTV, wanda zai ba mu karin haske kan motar da ake magana da yiwuwar gane masu laifin.
"Na tuntubi Lagas da ko'ina a rundunar don toshe dukkan hanyoyin fita daga jihar."

Kwastam sun kama muggan makamai a Ogun

A wani labarin, mun ji cewa jami'an hukumar kwastam reshen Ogun, sun kama harsasai da aka nade a cikin buhunan shinkafa biyar sannan aka boye su a wani jeji a hanyar Palace/Ayetoro da ke karamar hukumar Imeko Afon ta jihar.

An cafke kayan ne a ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba, bayan samun wasu bayanan sirri wanda ya kai ga tura wasu jami'ai yankin domin tinkarar wadanda ke shigo da makaman cikin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel