Tashin Hankali Yayin da Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke a Jihar Arewa

Tashin Hankali Yayin da Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke a Jihar Arewa

  • An samu asarar rayuka bayan ɓarkewar wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar Kebbi
  • Rikicin wanda ya auku a ƙaramar hukumar Suru ta jihar ya yi sanadiyyar rasuwar mutum biyu da raunata wasu mutum takwas
  • Gwamna Nasir Idris ya bayar da gudunmawar N13m ga iyalan waɗanda suka rasu da waɗanda suka samu raunuka a yayin rikicin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Rayukan mutum biyu sun salwanta yayinda wasu mutum takwas suka jikkata a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Suru ta jihar Kebbi.

Shugaban ƙaramar hukumar Suru, Mohammed Lawal, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba, a lokacin da yake zantawa da Gwamna Nasiru Idris, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun rutsa manoma a gonakinsu, sun yi ajalin mutum biyu har lahira a jihar Taraba

Mutum biyu sun rasu a rikicin makiyaya da manoma
Mutum biyu sun rasa rayukansu sakamakon barkewar rikicin makiyaya da manoma a Kebbi Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa rikicin ya faro ne da safiyar ranar Asabar, inda wasu manoma suka je gonakinsu suka tarar da makiyaya da shanunsu a gonakin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Manoman sun tambayi makiyayan ko su ne suke lalata amfanin gonakinsu wanda hakan ya haifar da rikici a tsakaninsu. An kashe mutane, an lalata dukiyoyi da gidaje."

Ya ce ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Kankure, Tunga Rimi, Tunga Mai Rakumi, Runhewan Dulmeru, Sabuwan Kendawa da Limarein.

Wane mataki gwamnan ya ɗauka?

Ahmed Idris kakakin gwamnan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Gwamna Nasir ya umurci shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (SEMA), Bello Rilisco, da ya zaƙulo wadanda abin ya shafa tare da tallafa musu da kayayyakin abinci da sauran kayayyakin agaji.

A kalamansa:

"Gwamna Nasiru ya shiga tsakani a cikin rikicin manoma da makiyaya a yankin Suru da Koko Besse na jihar domin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a cikin al’ummomin da rikicin ya shafa."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wa dakarun 'yan sanda wuta, sun halaka rayuka da yawa a jihar APC

"Ya kuma bayar da gudunmawar N13m ga iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka samu raunuka a rikicin."

Rikicin Manoma da Makiyaya Ya Barke a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla rayukan mutum 13 ne suka salwanta a wani rikicin manoma da makiyaya da ya ɓarke a ƙaramar hukumar Barikin Ladi ta jihar Plateau.

Lamarin dai ya auku ne bayan an yi wa wasu makiyaya su boyar kwanton ɓauna a yankin Rawuru cikin ƙaramar hukumar ta Barikin Ladi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel