Yan Boko Haram Sun Datse Kawunnan Mutane 11 Masu Sana’ar Itace a Borno

Yan Boko Haram Sun Datse Kawunnan Mutane 11 Masu Sana’ar Itace a Borno

  • Wasu 'yan bingiga haye akan rakuma da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kashe mutum sha daya da ke sana'ar itace a Borno
  • Lamarin wanda ya faru a yammacin ranar Litinin, rahotanni sun nuna cewa an yi wa mutanen sha daya yankan rago
  • Yan Boko Haram din sun yi wa mutanen zobe sa'ilin da suke aikin hada gawayi, inda suka kashe mutum shiga nan take

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Damboa, jihar Borno - Akalla masu sana'ar itace 11 ne aka ce wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suka sare kawunansu a karamar hukumar Damboa da ke jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin a kusa da Bale, wani kauye da ke a karamar hukumar Damboa.

Kara karanta wannan

Daga musayar magana: Ango ya kashe amaryarsa da surukarsa a ranar aurensu

Sojin Najeriya/Boko Haram/Jihar Borno
Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen na aikin hada gawayi, sa'ilin da 'yan Boko Haram suka zagaye su, inda aka kashe mutane shida nan take. Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Yadda lamarin ya faru

A cewar majiyoyin ‘yan banga na yankin, an gano gawarwakin wadanda lamarin ya rutsa da su a wata gona da misalin karfe 5 na yamma, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce:

“Eh, an gano gawar mutane shida a gonar da lamarin ya faru da yammacin jiya (Litinin) kuma domin an anyi gunduwa-gunduwa da sassan jikinsu.
“Mun yi jana’izar su da yammacin yau kamar yadda addinin musulunci ya tanadar. Ko da yake mutane biyar sun bace, ba mu sani ba ko sun tsere ko anyi garkuwa da su."

Wani jigo a kungiyar ‘yan bangar ya bayyana cewa, mutanen na aikin hada gawayi, sa'ilin da 'yan Boko Haram suka yi masu zobe, inda aka kashe mutane shida nan take.

Wanda ya kubuta daga harin ya ba da labari

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri, Tinubu na da shirin ciyar da kasar nan gaba, shawarin minista ga 'yan Najeriya

Majiyar ta ce:

“Sun zo a kan rakuma suka kewaye mu, sun kai kusan 15, ni dai na samu damar tserewa, suka bi bayana. Allah ya taimakeni na san hanyar da kyau na tsere musu.
“Daga baya, mun tattara mutane muka je wurin da lamarin ya faru. Nan muka taras da gawarwakin mutum shiga, amma ba mu ga sauran mutum biyar ba.
“A safiyar yau ne muka sake gano karin gawarwakin mutum biyar don haka muna da gawarwakin mutum goma sha daya kenan. "

Yan sanda sun kama wanda ya dau nauyin mata suyi zanga-zanga zigidir

A safiyar yau, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kama wanda ake zargi da daukar nauyin matan da suka fito zanga-zanga zigidir a jihar Anambra.

Wanda ake zargin, Ozo Jeff Nweke, a cewar rundunar 'yan sanda an kama shi ne a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel