Watan Ramadan: hanyoyi 20 na haddace Alkur'ani

Watan Ramadan: hanyoyi 20 na haddace Alkur'ani

-  Al kur'ani mai girma, tare da hadisan manzon Allah( tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) su ne magudanar rayuwan musulmi.

-  Littafin Allah shine kundin tsarin rayuwar musulmai, wanda aka saukar wa musulmai domin ya zama shiriya garesu kuma da rahama.

-   A watan Ramadana, da yawa daga cikin mutane za su dujufa da karatun Alkura'ani , yayinda wa su kuma za su dinga haddace shi

Allah ya nuna girman Alkur'ani a cikin Alkur'anin .

Allah ya ce a Suratul Baqara aya ta 2 :" Wannan ne littafin ,wanda babu kokwanto a cikin ta, shiriya ce ga masu tsoron Allah". A surah ta 17 , aya ta 82 , Allah yace:" Kuma mun saukar Alkur'ani wacce take waraka ne da rahama ga muminai, kuma bata karawa kafirai koma sai bata".

Manzon Allah yayi bayanin muhimmancin alkur'ani , ya fadi a hadisi ingantacce cewa:" mafi Alkhairi a cikin ku, shine wanda ya iya Alkur'ani kuma ya koyar da shi".

A wata kaulin manzon Allah , yace Alkur'ani zata yi shafa'a ga makarantanta a ranar gobe kiyama.

Ka biyo mu ka ga hanyoyi masu sauki na iya handacce Alkur'anim

1. Tabbatar da tauhidi (kadaita Allah)

2. Tsarkake zuciya da yin niyya mai kyau ( wato yi domin Allah)

3. . Yawan ambaton Allah.

4. Yawan neman gafara a wajen ubangiji.

5. Gujewa miyagun halaye.

6. Zaban takamanman lokaci domin haddace Alkur'ani

7.samun abokin na kwarai da zai taimaka wajen yi tare

8. Kada kuma ka bari hadda ya hanaka karatun Alkur'ani, kada ya kasance hadda zalla kakeyi

9. Ka samu lokacin karanta tafsirin ayoyin da ka haddace

10. Banda hanzari

11. Samun malamin da zai koyar da kai

12. Yin amfani da Alkur'ani dayal kacal takamanmai na hadda.

13. Karanta ayioyin da ka haddace a cikin sallah.

14.Tashi sallan dare

15. Tabbatar da cewa Alkur'ani itace kan gaba

14. ladabtar da kanka idan ka ki yadda kmya kamata ( shi yasa 11 na da muhimmanci(

17. Sannin ka'idojin hadda

18. Kawar da girman kai da wasu munanan halaye.

19. Kasancewa a tsarkake kuma cikin alwala kafin hadda

20. Sanin cewa haddat Alkur'ani shine mataki na farko wajen neman ilimi

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng