Luguden Wuta: Sojoji Sun Kai Samame Maɓoyar Yan bindiga a Garuruwa 6, Da Yawa Sun Sheka Lahira

Luguden Wuta: Sojoji Sun Kai Samame Maɓoyar Yan bindiga a Garuruwa 6, Da Yawa Sun Sheka Lahira

  • Yan bindiga sun mutu yayin da sojoji suka kai farmaki kan sansanin yan ta'adda a kauyuka da dama a jihar Zamfara
  • Mai magana da yawun rundunar Operation Hadarin Daji, Kaftin Yahaya Ibrahim ya ce sojoji sun raba yan bindiga hudu da duniya
  • Acewarsa, dakarun sun kwato shanu 57 na sata, kayan sojoji da makudan kuɗi da suka kai Naira 900,000 daga hannun yan ta'addan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadarin Daji da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Arewa maso Yamma sun kashe ‘yan ta’adda hudu a Zamfara.

Sojoji sun samu nasara kan yan bindiga a Zamfara.
Dakarun Sojoji Sun Halaka Yan Bindiga, Sun Kwato Shanun da Suka Sace a Zamfara Hoto: channelstv
Asali: UGC

Dakarun sojin sun samu wannan nasara ne a wani samamen share ƴan ta'ada da suka kai maɓoyar ƴan bindigan, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan hari garuruwa 4 a arewa, sun tafka ɓarna tare da sace mutum 150

Sojojin sun kai farmaki ne kan wasu sansanonin ƴan ta'adda da suka gano a kauyukan Tazame, Mashema, Gandaya, Maje, da kuma Doka a ƙaramar hukumar Bungudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma ba su tsaya nan ba, sun kai samame kan wata maɓoyar ƴan bindiga a dajin da ya kewaye kauyen Gandaya a wannan ƙaramar hukumar ta Zamfara.

Mai magana da yawun rundunar Operation Hadarin Daji, Kaftin Yahaya Ibrahim ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba.

Ya ce wasu 'yan ta'adda da ba a tabbatar da adadinsu ba sun tsere dauke da raunukan harbin bindiga yayin samamen baya-bayan nan da aka kai.

Sojoji sun kwato kayayyaki da dama

Kaftin Ibramin ya ce:

"Sojojin sun kwato shanu 57 da aka sace, kayan aikin soja, kayan barci da Naira dubu dari tara (tsabar kuɗi) daga hannun ‘yan ta’addan a wannan samame."

Kara karanta wannan

PDP ta kara shiga matsala yayin da kotun daukaka kara ta tsige yan majalisa 11 a jihar Filato

"Dukkan wuraren da aka gano yan bindiga na samun mafaka da sansanin da sukw kasuwanci an lalata su gaba ɗaya."

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugaban APC a Neja

A wani rahoton na daban kuma ƴan bindigan sun yi garkuwa da tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Wushishi, jihar Neja, Alhaji Sule Muhammad.

Ƴan bindiga sun kutsa cikin garin da sanyin safiyar ranar Alhamis, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi kafin daga bisani suka yi awon gaba da ɗan siyasan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262