A Karshe, Tinubu Ya Koma Aso Rock Bayan Shafe Watanni 2 A Asokoro Don Rage Cunkoso

A Karshe, Tinubu Ya Koma Aso Rock Bayan Shafe Watanni 2 A Asokoro Don Rage Cunkoso

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya koma cikin fadar shugaban kasa bayan shafe watanni biyu a Asokoro
  • Tinubu ya koma fadar ne saboda yawan korafi na mutane akan cunkoso da shugaban ke jawo wa a birnin Abuja
  • Wata majiya ta tabbatar cewa Shugaba Tinubu ba ya jin dadin yadda ya ke takurawa talakawa shi yasa ya koma fadar

FCT, Abuja - A karshe shugaban kasa, Bola Tinubu ya koma fadarsa ta Aso Rock a ranar Lahadi 30 ga watan Yuli da dare.

Shugaba Tinubu kafin komawarsa ya na zaune ne a gida na musamman da ke Asokoro a birnin Abuja bayan shafe watanni biyu tun bayan rantsar da shi.

Shugaba Tinubu ya koma Aso Rock don takaita cunkoso a hanyoyin Abuja kamar yadda ake korafi
ShugabaTinubu Ya Ji Korafin Jama'a Akan Cunkoso Da Ya Ke Jawowa A Titunan Abuja, Koma Fadarsa. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Tinubu ya ji korafin jama'a kan jawo cunkoso a Abuja

Tinubu ya koma gidan gilashi da ke fadar kafin kammala gyaran ainihin gidan da shugaban kasa ke zama a hukumance.

Kara karanta wannan

Jar miyan matasa: Tinubu zai sama wa 'yan Najeriya aiki a Google, ya fadi ta yaya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan korafi daga al'umma yadda shugaban ke jawo cunkoso a hanyoyin birnin da kuma yawan tare hanyoyi da ake yayin da ya ke fitowa.

Wata majiya a fadar shugaban kasa ce ta bayyana haka ga TheCable inda ta ce an dauki matakin ne don saukakawa mutane.

An bayyana ranar da za a kammala gyaran fadar shugaban

Ta ce:

"A karshe, ya koma a jiya Lahadi da dare bayan korafi na mutane akan yawan cunkoso da ya ke jawo wa a titunan birnin.
"Shi kansa ba ya jin dadin takurawa al'umma, duk da cewa gidansa a hukumance bai kammala ba, ya yanke shawarar komawa gidan gilashi a fadar."

Rahotanni sun tabbatar cewa za a kammala gyaran gidan shugaban kasan a watan Agusta mai kamawa, cewar TheCable.

A shekarar 2015, shugaba Buhari ya shiga gidan makwanni uku kacal bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Tinubu Na Ganawar Sirri Da Shugaban Kasar Benin, Patrice Talon

Ministocin Tinubu: Ainihin Dalilin Da Yasa Aka Zabi Wike Ya Fito Fili

A wani labarin, tsohon minista, Sanata Adeseye Ogunlewe ya bayyana dalilin da yasa Tinubu ya ba wa Wike mukamin minista

Adeseye ya ce Tinubu ya ba shi mukamin ne don saka masa akan irin gwagwarmayar da ya yi.

Sanatan ya ce Wike ya cancanci hakan bayan bijirewa jam'iyyarsa ta PDP da ya yi da kuma yi wa APC aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel