“Babu Rana”: Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Lokacin da Kotu Zata Yanke Hukuncin Zaben Abba Gida-Gida

“Babu Rana”: Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Lokacin da Kotu Zata Yanke Hukuncin Zaben Abba Gida-Gida

  • Gwamnatin Kano ta magantu a kan rahotannin da ke yawo game da ranar yanke hukunci a shari'ar zaben gwamnan jihar
  • Babban sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature ya ce har yanzu babu wata rana ko lokaci da kotun daukaka kara ta tsayar don yanke hukunci
  • Ya bukaci jama'a da su daina yada labaran karya cewa kotu na da ikon yanke hukunci a duk san da ta ga dama cikin lokacin da doka ta tanadar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano, ta yi watsi da rahotannin da ke sanar da ranar da kotun daukaka kara zata yanke hukunci a shari'ar Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP da Nasir Gawuna na APC.

Kara karanta wannan

Kano: Primate Ayodele ya aika sakon gargadi ga Abba Gida-Gida yayin da kotu ke shirin yanke hukunci

Tun a farkon makon nan ne rahotanni suka dungi yawo cewa ana zaman dar-dar a jihar Kano saboda shirin da kotun daukaka karar ke yi na yanke hukunci a shari'ar zaben gwamnan na 2023.

Gwamnatin Kano ta ce babu ranar yanke hukunci a shari'ar Abba
“Babu Rana”: Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Lokacin da Kotu Zata Yanke Hukuncin Zaben Abba Gida-Gida Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Harma mun ji cewa rundunar yan sanda na jihar ta kara tsaro yayin da ake shirin yin hukunci a shari’ar zaben Gwamna a garin Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Litinin, Leadership ta ce rundunar ‘yan sandan reshen Kano ta shaida cewa an baza dakaru zuwa wurare na musamman.

Babu bayani dangane da ranar yanke hukuncin Kano, Gwamnatin Kano

Sai dai kuma, wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature, ya fitar a shafinsa na X (wanda aka fi sani da twitter a baya) a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, ya jaddada cewa har yanzu ba a tsayar da ranar yanke hukunci ba.

Kara karanta wannan

Yanzu yanzu: Kotun daukaka kara na shirin yanke hukunci a karar da ke neman tsige gwamnan APC

Ya bukaci jama'a da su guji yada labaran karya yana mai cewa kotu na da damar sanya rana da lokacin yanke hukunci a duk san da ta ga dama cikin lokacin da doka ta tanadar.

Ya ce:

"Babu wani bayani da aka fitar dangane da batun ranar yanke hukuncin Kano a kotun daukaka kara har ya zuwa yanzun nan...
"Kotu na damar sanya rana da lokacin yanke hukunci a duk lokacin da ta ga dama cikin wa'adin da doka ta tanadar.....
"Muna fatan alkhari a koda yaushe....
"Sabature."

Ayodele ya magantu kan shari'ar zaben Kano

A wani labarin, mun ji cewa Primate Elijah Ayodele ya shawarci Abba gida-gida da ya tashi tsaye da addu'a gabannin yanke hukuncin da kotun daukaka kara za ta yi a shari'ar zaben gwamnan jihar Kano.

Malamin addinin ya ce idan har gwamnan na Kano na so ya yi nasara a kotun daukaka kara, toh sai ya nemi taimakon Allah.

Abba dai yana kalubalantar hukuncin kotun zabe da ta tsige shi daga kujerarsa a kotun daukaka kara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel