An Shiga Dar-Dar Yayin Jiran Hukuncin Zaben Gwamna a Jihohin Kano da Filato

An Shiga Dar-Dar Yayin Jiran Hukuncin Zaben Gwamna a Jihohin Kano da Filato

  • Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna suna shari’a a kan zaben Gwamnan jihar Kano a kotun daukaka kara
  • Shi ma Gwamnan Filato watau Gwamna Caleb Mutfwang ya na kokarin tsare kujerarsa a babban kotun kasar
  • Jam’iyyar PDP ta rasa kujerun ‘yan majalisar tarayya yadda kotun korafin zabe ta fara tsige NNPP daga mulkin Kano

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ana sa ran kotun daukaka kara za tayi hukunci a shari’o’in zaben Gwamnonin jihohin Filato da Kano kafin karshen mako.

Rahoton Daily Trust ya ce magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da mutanen Nasiru Yusuf Gawuna suna ta fatan samun nasara a kotun.

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano da mataimakinsa Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Yadda abubuwa su ke bayan zaben Kano

A baya kotun sauraron karar zaben Kano ta ce Nasir Yusuf Gawuna ne halataccen Gwamna da aka zaba, ta tsige Abba Kabir Yusuf da NNPP.

Kara karanta wannan

Kano: Primate Ayodele ya aika sakon gargadi ga Abba Gida-Gida yayin da kotu ke shirin yanke hukunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ake jiran a ji hukunci, an ji jami’an tsaro sun tsaurara matakai a jihar Kano.

...Jam'iyyar PDP ta tsure a Jihar Filato

A jihar Filato kuwa, kotun sauraron karar zaben ta tabbatar da kujerar Gwamna Caleb Mutfwang, amma an tsige sauran ‘yan majalisan PDP.

Da aka je kotun daukaka kara, Sanatoci da ‘yan majalisar wakilan tarayya na PDP sun rasa kujerunsu, hakan ya tada hankalin jam’iyyar.

Nasarar da kotun zabe su ka ba APC ta jawo zanga-zanga a wasu wurare a Filato. Jihar na da tsohon tarihin rikici kabilanci da na addini.

Kano: Kujerun NNPP sun dawo

A Kano akasin hakan ta faru a kotun daukaka kara, alkalai sun dawowa jam’iyyar NNPP kujerun da aka karbe mata a shari’ar majalisar tarayya.

Kano ta yi suna a tarihi wajen siyasa mai zafi tun daga lokacin Sardauna da Aminu Kano, zuwa siyasar jamhuriyya ta biyu har zuwa halin yanzu.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta shirya raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan APC a jihar Arewa

Galabar da NNPP ta yi wajen karbe kujerun Tarauni, Kura-Garun Malam-Madobi, Kumbotso da sauransu ya ba jam’iyyar kwarin gwiwa sosai.

Sai dai duk da haka masu goyon bayan APC da Gawuna sun dage da addu’o’i domin babban kotun ta tabbatar da irin hukuncin kotun korafin zabe.

Kano da shari'o'i masu ban mamaki

Rahoto ya zo cewa a karon farko a tarihin siyasa kotu ta tsige Gwamna watau Abba Kabir Yusuf saboda rashin sa hannu da hatimi a kuri’un NNPP.

A Filato, 'yan majalisu biyar aka tsige, kotun zabe sun tsige Sanata da ya samu kuri’u fiye da 90, 000, aka mika kujerar ga wanda ya ci kuri’u 40,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel