Babban Rashi Yayin Da Mace Manjo Janar Ta Farko a Najeriya Ta Riga Mu Gidan Gaskiya Ta Na Shekaru 84

Babban Rashi Yayin Da Mace Manjo Janar Ta Farko a Najeriya Ta Riga Mu Gidan Gaskiya Ta Na Shekaru 84

  • Ana cikin jimami yayin da mace ta farko da ta zama Manjo Janar a soja ta riga mu gidan gaskiya a birnin Landan
  • Manjo Janar Aderonke Kale mai ritaya ta rasu a ranar Laraba 8 a watan Nuwamba bayan fama da doguwar jinya
  • E. O Okafor, shugaban hukumar AANI shi ya bayyana haka a jiya Alhamis 9 ga watan Nuwamba a Landan da ke Ingila

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Rundunar sojin Najeriya ta yi babban rashi yayin da mace ta farko da ta fara zama Manjo Janar ta riga mu gidan gaskiya.

Marigayiyar mai suna Aderonkre Kale ta rasu a ranar Laraba 8 ga watan Nuwamba ta na da shekaru 84 a duniya, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Dakarun soji sun damke wasu motoci 3 da ake zargi a zaben jihar Kogi

Manjo Janar ta farko a Najeriya ta riga mu gidan gaskiya
Kale ta rasu ne a birnin Landan da ke Ingila. Hoto: @toluogunlesi.
Asali: Twitter

Yaushe Kale ta rasu?

E. O Okafor, shugaban hukumar AANI shi ya bayyana haka a jiya Alhamis 9 ga watan Nuwamba a Landan da ke Ingila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

TheCable ta tattaro cewa tsohon kakakin rundunar sojin, S. K Usman ya fitar da sanarwa kan rasuwar Kale.

Sanarwar ta ce:

“Tabbas Najeriya ta yi babban rashi na Manjo Janar Aderonke Kale mai ritaya wacce ta ba da gudunmawa a bangaren lafiya da kuma rundunar a kasar.

Wacece Kale a Najeriya?

An haifi Kale a ranar 31 ga watan Yuli na shekarar 1939 ta kuma kamala kararun aikin likitanci a Jami’ar Ibadan da ke jihar Oyo.

Daga bisani ta samu horon likitanci na warkar da mahaukata a a Jami’ar Landan da ke Burtaniya.

Marigayiyar ta kuma yi aiki a Burtaniya kafin dawo wa Najeria ta shiga rundunar soji a shekarar 1972.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da aka kama wani da kokon kan mutum sabon yanka a Ibadan, hotuna sun bayyana

Ta zama Kanal da kuma mataimakiyar kwamandan sojin Najeriya a shekarar 1990 da kuma 1994.

Ta samu Karin girma zuwa mukamin Manjo Janar yayin da ta yi ritaya daga rundunar sojin a shekarar 1997.

Ana saura kwana 1 zabe, dan siyasa ya mutu a Kogi

A wani labarin, awanni kadan kafin gudanar da zaben gwamna a jihar Kogi, shahararren dan siyasa ya mutu a jihar.

Marigayin mai suna Muhammad Danasabe shi ne shugaban karamar hukumar Lokoja kafin rasuwarshi a yau Juma’a 10 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel