Sojoji Zasu Yi Juyin Mulki a Najeriya? Babban Hafsan Tsaro CDS Musa Ya Yi Bayani

Sojoji Zasu Yi Juyin Mulki a Najeriya? Babban Hafsan Tsaro CDS Musa Ya Yi Bayani

  • Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya kore yiwuwar juyin mulki a ƙasar nan
  • Yayin wata ziyara da ya kai hedkwatar sojoji a Patakwal, CDS ya ce sojojin Najeriya zasu tsaya tsayin daka wajen kare tsarin demokuraɗiyya
  • A cewarsa, duk da abin da ke faruwa a wasu ƙasashen da ke maƙotaka da Najeriya, sojoji ba zasu kwatanta juyin mulki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Rivers - Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya yi watsi da yiwuwar juyin mulki a Najeriya.

Hafsan tsaron ya tabbatar da cewa rundunar sojin na goyon bayan tsarin demokuraɗiyya a ƙasar nan, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Christopher Musa.
Tinubu: CDS Christopher Musa Ya Kore Yuwuwar Juyin Mulki a Najeriya Hoto: NigerianArmy
Asali: Facebook

Janar Musa ya bayyana haka ne yayin da yake hira ga ƴan jarida lokacin da ya kai ziyarar aiki ta farko ga rundunar sojin ƙasa ta 6 mai hedkwata a Patakwal, jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: Luguden wutar sojojin Najeriya ya halaka ƴan ta'adda sama da 160 a jihohin arewa 2

Ya kuma ƙara tabbatar wa ƴan Najeriya cewa jami'an soji sun duƙufa wajen yin duk mai yuwuwa a kokarin kare martabar mutanen ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A zahirin gaskiya na fara kewaya wa ne, na fara daga jihar Imo na je Bayelsa, yanzu gani a Jihar Ribas duk a kokarin karfafa wa sojoji gwiwa su ƙara jajircewa da nuna kwarewa a aiki."
"Muna son ƴan Najeriya su samu tabbacin cewa dakarun soji na tare da su, mun shirya kare su da kare demokuraɗiyya, za kuma mu tabbatar demokuraɗiyya ta samu gindin zama."
"Bamu son kowa ya sa fargaba a ransa, mun ga yadda juyin mulki ya zama ruwan dare a Afirka, a kasashen da ke kusa da Najeriya kamar Burkina Faso da Nijar da Mali."
"Na san ana cikin fargaba da ɗar-ɗar, ina mai tabbatar wa kowane ɗan ƙasa cewa sojoji sun sadaukar da kansu da jajircewa wajen tabbatar da tsaro, goyon baya da tsaya wa kan tsarin demokuraɗiyya."

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun yi fatali da tsagin Atiku, sun koma goyon bayan shugaba Tinubu kan abu 1 tak

- CDS Musa.

Matakan da sojoji suka ɗauka

Babban hafsan tsaron ya kara da cewa tuni suka fara ɗaukar matakan da ya dace domin kawo ƙarshen satar ɗanyen mai a yankin Neja Delta.

A cewarsa, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ware wasu kuɗaɗe domin tanadar kayan aikin da zasu taimaka wa sojoji wajen kawo karshen satar mai, The Nation ta ruwaito.

Sojoji sun ragargaji Boko Haram

A wani rahoton kuma Rundunar sojin saman Najeriya na Operation Hadin Kai ta halaka ƴan ta'adda sama da 160 a wani samame ranar 2 ga watan Nuwamba.

An ce jirgin yaƙin NAF ya saki ruwan bama-bamai kan mafakar Boko Haram biyu a Yobe da Borno, sojoji ƙasa suka mara masa baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel