Dakarun Sojoji Sun Bankaɗo Wani Shiri, Sun Yi Kakkausan Gargaɗi Kan Zaben Gwamna a Jihohi 3

Dakarun Sojoji Sun Bankaɗo Wani Shiri, Sun Yi Kakkausan Gargaɗi Kan Zaben Gwamna a Jihohi 3

  • Rundunar soji ta sake sabon gargaɗi bayan gano wasu gurɓatattu na shirin yin shigar sojoji a zaɓen gwamna da ke tafe a jihohi uku
  • Kakakin rundunar, Edward Buba, ya ce dakaru sun shirya raunata duk wanda ya yi yunkurin tada zaune tsaye lokacin zaɓen
  • Ya ce sun girke jami'an tsaro a wurare daban-daban domin banbance sojojin gaskiya da na ƙarya

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta sake gargaɗi da babban murya ga duk waɗanda ke yunƙurin tada zaune tsaye a zaɓukan gwamnonin da za a yi a jihohin Imo, Kogi da Bayelsa.

Sojoji sun gargaɗi masu shirin tada zaunr tsaye.
Dakarun Soji Sun Fitar da Sabon Gargadi Ga Masu Shirin Tada Yamutsi a Jihohi 3 Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Rundunar ta ce dakarun sojojin da ta tura jihohin guda uku zasu raunaka dun wanda ya yi yinƙurin kawo cikas a zaɓen da ke tafe, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Imo: Akwai yiwuwar ba za a yi zabe ba bayan an samu sabani kan muhimmin abu 1

Ta ce tana sane da shirin wasu mutane na yin shigar sojoji don kawo cikas ga harkokin zabe a jihohin uku a ranar Asabar yayin zaben gwamnoni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa ta Najeriya, Edward Buba, ne ya yi wannan bayanin yayin da yake jawabi ga ƴan jarida a Abuja ranar Alhamis.

Ya ce jami'an soji sun shirya tsaf domin tabbatar da tsaro da kuma gudanar da zaɓen cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Rundunar soji ta bankado shirin wasu gurɓatattu

Buba ya ce:

“Ku nisanci zaben gwamna da za a yi ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa ko kuma ku fuskanci mummunan sakamako daga sojoji. Muna da labarin kuna shirin sa kayan sojoji ku yaudari jama'a."
"Muna tabbatar muku zaku gamu da sakamakon raunuka idan kuka aiwatar da shirinsku, ba zamu yarda a ɓata sunan sojoji ba, ku shiga taitayinku, muna ƙara gargaɗin ku."

Kara karanta wannan

Babban labari: Farashin Litar man fetur ya ƙara tashin gwauron zabi a jihar APC, An shiga wani hali

A cewarsa, an tura dakarun sojoji zuwa wurare daban-daban domin karfafa matakan tsaro da aka riga aka kafa a jihohin.

Ya ce hukumomin tsaro sun shirya yadda zasu banbance tsakanin sojojin gaske da na bogi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Gwamnan Zamfara ya aike da saƙo ga hukumomin tsaro

A wani rahoton kuma Dauda Lawal ya yi kira ga hukumomin tsaro su ƙara danƙon hadin kai a tsakanin su domin tabbatar da tsaro a Zamfara.

Gwamnan ya bayyana cewa tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma ne babban abin da ya sa gaba a gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel