Yan daukar amarya 30 sun gamu ajalin su a jihar Sokoto
Labaran da muke samu da dumi dumin sa na nuna mana cewa kimanin yan daukar amarya 30 ne suka gamu da ajalin su a jihar Sokoto ta sanadiyyar wani mummunan hadarin moto a kan hanyar su ta zuwa Kware daga Gwadabawa.
Kamar dai yadda muka samu labarin, hadarin ya auku ne a tsakanin wata babbar mota da kuma wata motar alfarma kirar kirar Toyota Spora wadda take shake da yan daukar amarya da amaryar kanta kimanin karfe 8 na safe a ranar Lahadin da ta gabata.
KU KARANTA: Auren yan fim 6 ya mutu a wannan shekarar
Legit.ng ta samu dai cewa wani ganau ya shaidawa majiyar mu yadda abun ya faru inda ya bayyana cewa tayar babbar motar ce ta fashe inda tayiyo kan motar alfarmar dauke da yan daukar amaryar ta kuma latse ta.
To sai dai da aka tuntubi jami'in hukumar kiyaye hadurra ta kasa shiyyar jihar Aliyu Kanya ya bayyana cewa matsanancin gudu ne ya jawo hadarin kuma rayuka 20 ne suka salwanta yayin da wasu 12 suka ji munanan raunuka.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng