Hukumar EFCC tayi diran mikiya akan babban alkalin Najeriya Walter Onnoghen, Fayose, Fayemi da sauransu
- Hukumar EFCC ta fadada bincike zuwa manyan ma'aikatan gwamnati da yan siyasa
- Cikin wanda hukumar ke gudanar da bincike akai sun hada da gwamna Fayose, Walter Onnoghen, Kayode Fayemi, Ngozi Okonjo-Iweala da wasu manyan mutane
- Sunayen mutanen da hukumar ke bincike sun kai guda 100
Hukumar EFCC tace babban alkalin Najeriya, Walter Onnoghen; gwamna Ayodele Fayose, ministan ma'adinai Kayode Fayemi; da kuma tsohuwar ministan kudi, Ngozi Okonjo-Iweala duk suna cikin manyan mutane da hukumar ke gudanar da bincike akansu.
A cewar jaridar Punch, sunayen dai suna cikin wata takarda ne da ke dauke da sunaye guda 100 na manya-manyan yan siyasa da kuma ma'aikatan gwamnati da hukumar ke gudanar da bincike akan su a watan Augusta na 2017.
Jami'in jaridar Punch ya ga takardan ne a ranar Litinin bayan ofishin ministan shariah, Mr Abubakar Malami (SAN) ya nemi hukumar EFCC din ta aika masa da takardan.
A cewar jami'in jardidar Sunday Punch, akwai sunayen tsofafin gwamnoni wanda a yanzu wasun daga cikin su ministoci ne da kuma yan majalisa a gwamnatin shugaba Buhari. Wasu daga cikin mutanen ana bincikan su a dalilin badakalan siyan makamai na dallan Amurka 2.1.
DUBA WANNAN: Gwamna Fayose baya kaunan musulmai, shigar musulunci da yayi isgili ne kawai - MURIC
A cikin sunayen manyan mutanen da ake gudanar da bincike kansu harda gwamnan jihar Kogi mai ci yanzu, Yahaya Bello da kuma tsohon gwamnan jihar Captain Idris Wada.
Sauran tsofafin gwamnonin sun hada da Godswill Akpabio na jihar Akwa Ibom, Jonah Jang na jihar Plateau, Ali Modu Sheriff na jihar Borno da kuma Lucky Igbinedion na jihar Edo.
Akwai kuma sunan Dame Patience Jonathan, uwargidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da wasu ministoci da sukayi aiki a karkashin gwamnatin Jonathan.
Bayan Okonjo-Iweala, wasu tsofafin ministocin da ke takardan sun hada da Mrs. Diezani Alison-Madueke da kuma maigidanta Rear Admiral Alison Madueke (mai ritaya), Mr Mohammed Adoke (SAN), Bala Mohammed, Mrs. Stella Oduah da kuma Godsday Orubebe.
Har ila yau, an gano sunayen mataimakan tshohon shugaba Jonathan akan kafafen yadda labari Dr. Rueben Abbati da kuma Dr. Doyin Okupke.
Sauran manya mutanen da sunayen su ke takardan harda tsohon Comptroller janar na kwastam, Abdullahi Dikko, tsohon shugaban rikon kwaryan PDP, Uche Secondus, Col. Bello Fadile (mai ritaya), Sambo Dasuki, Alkali Abdu Kafarati da kuma Alkali Mohammed Tsamiya.
Hukumar EFCC tace ta samu bayanan sirri ne daga masu tonan asiri da kuma koke-koken da mutane ke rubutawa zuwa ga hukumar.
A cikin takardan, akwai ranakun da hukumar ta fara bincike akan wadanda ake zargi da laifin.
Mai magana da yawun Fayose, Lere Olayinka yace zasu fara ba EFCC hadin kai idan ta fara aiki kamar yadda ya dace.
Fayose yace sun shigar da karar gwamna Koyode Fayemi ga hukumar amma basu yi komi akai ba.
Yan jarida sun kasa ji ta bakin mai magana da yawun babban alkalin kasa, Awassam Bassey domin wayar sa na kashe.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng