Kisan Janar Alkali: An Samu Ci Gaba Yayin da Lauyan Mai Kara Ya Gabatar da Muhimmiyar Shaida

Kisan Janar Alkali: An Samu Ci Gaba Yayin da Lauyan Mai Kara Ya Gabatar da Muhimmiyar Shaida

  • An ci gaba da karbar shaidu a shari’ar da ake yi na kisan gillar da aka yi wa Janar Muhammad Alkali a jihar Plateau
  • Lauya mai gabatar da kara, Simon Mom ya gabatar da shaida a rabuce na Chuwang Timothy da ake zargi da hannu a ciki
  • Marigayi Janar Alkali dai ya gamu da ajalinsa a wani kauye a Jos ta Kudu yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau – Yayin da ake ci gaba da shari’ar kisan Janar Alkali, lauyan mai kara ya gabatar da muhimmiyar shaida a rubuce a gaban kotu.

Lauyan ya gabatar da shaidan ne a ranar Talata 7 ga watan Nuwamba na daya daga cikin wadanda ake zargi, Timothy Chuwang a rubuce.

Kara karanta wannan

Ana saura kwanaki 3 zaben gwamna, a karshe tsohon shugaban kasa ya bayyana wanda ya ke muradi

Lauya mai gabatar da kara ya gabatr da shaida a rubuce na wanda ake zargi
Kisan Janar Alkali: Ana ci gaba da sauraran shari'ar kisan a Plateau. Hoto: Nigerian Army.
Asali: UGC

Yaushe aka yi ajalin alkali a Plateau?

Idan ba a mantaba an hallaka Janal Alkali Muhammad ne a ranar 3 ga watan Satumba na shekarar 2018 a kauyen Dura Du da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Timothy na daga cikin wadanda su ka hada baki wurin yi wa Janar din kisan gilla yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja.

Lauyan mai kara, Simon Mom ya gabatar da Comfort Idi wacce Sifeta ce ta ‘yan sanda daga bangaren binciken manyan laifuka, cewar Daily Trust.

Wane shaida aka gabatar kan kisan Alkali?

Yayin sauraran shari’ar, Comfort ta tabbatar wa alkalin kotun, Mai Shari’a, A. Ashom cewa Timothy ya amsa laifukan a rubuce.

Har ila ayu, ta ce an fassara wa Timothy abin da ya fada da harshen Hausa inda ya tabbatar ya fahimci komai kuma ya rattaba hannu a kai.

Kara karanta wannan

Mai magani ya dirkawa wani harsashi har lahira yayin gwada maganin bindiga a Bauchi

Ta kuma kara da cewa, mai gidanta a wurin aiki, Mangsok Tikop wanda ya yi ritaya ya tabbatar da cewa shi ma ya na da kwafin amsa laifukan wanda ake zargin, Trust Radio ta tattaro.

Alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraran shari’ar har sai zuwa 7 ga watan Disamba na wannan shekara da mu ke ciki.

Ana ci gaba da sauraran shari’ar Janal Alkali a Jos

A wani labarin, an ci gaba da sauraran shari’ar kisan gillar da aka yi wa Janar Alkali a jihar Plateau a shekarar 2018.

An hallaka Janar din ne a wani kauye da ke karamar hukumar Jos ta Kudu da ke jihar a kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel