Takaitaccen tarihin Janar Idris Alkali

Takaitaccen tarihin Janar Idris Alkali

An haifi Marigayi Janar Idris Alkali a garin Potiskum Jihar Yobe a shekarar da Nigeria ta samu 'yan cin kai wato 1960, bayan ya kammala karatun sakandare ya samu gurbin shiga babban makarantar sojoji na NDA da ke Kaduna a shekarar 1980.

Bayan Janar Idris Alkali ya kammala karatu da karban horo a NDA an karramashi da mukamin mataimakin laftanar (Second lieutenant) a shekarar 1983.

Daga nan aka kaishi ya fara aiki a bangaren sojojin da suka kware a yakin sunkuru (Infantry Corps) amma bai jima ba sai aka kaishi bangaren kwararru masu tattara bayanan sirrin tsaro (Intelligence Corps).

Takaitaccen tarihin Janar Idris Alkali
Takaitaccen tarihin Janar Idris Alkali
Asali: Twitter

Marigayi Janar Idris Alkali yana da matakin karatun shaidar digiri na biyu (Masters degree) wanda yayj a jami'ar tsaro ta kasar Amurka (National Defense University in Washington DC).

Wato yana da digiri na biyu a bangaren ilmin tsaro wanda yayi a makarantar koyon yaki (National War College) dake Amurka, sannan sai wani digiri na biyu a kan tsaro da dabarun yaki a makarantar College of International Security Affairs.

KU KARANTA: Kungiyar Shi’a ta saki jerin sunayen mambobinta 34 da Sojoji suka kashe

Yana da shaidar wanda ya kammala karatun digiri a bangaren magance ayyukan ta'addanci a duniya (International Counterterrorism) a NDU, sannan yana da digiri akan ilmin yaki (War Studies) wanda yayi a kasar Pakistan (University of Baluchistan, Quetta, Pakistan), sannan yayi Postgraduate Diploma akan mu'amalar kasashen duniya (Diplomatic Studies) daga jami'ar Westminster dake kasar Burtaniya (University of Westminster, London, UK)

Takaitaccen tarihin Janar Idris Alkali
Takaitaccen tarihin Janar Idris Alkali
Asali: Facebook

Janar Idris Alkali yayi ritaya a matsayin babban mai kula da tsare-tsare (Admin) na rundinar sojin Nigeria.

Al'ummar mahaifarshi Potiskum sunce yayi sanadin shigar da dunbin matasa aikin soji, mutum ne mai gaskiya da amana da saukin, kai bashi da girman kai, duniya bata dameshi ba, duk lokacin da yaje hutu garinsa Potiskum idan ka ganshi yana zaune a waje ba zaka taba tsammanin babban hafshin soji bane.

Janar Idris Alkai Ya hadu da ajalinsa a hannun mugayen maguzawan 'yan ta'addan kabilar berom ranar 3-9-2018 da misalin karfe 12 zuwa tsakanin karfe 1 na rana, a garin Dura-Du kudancin Jos Jihar Pilato kan hanyarshi na zuwa Bauchi domin ya duba gonarsa kafin ya wuce garinsa Potiskum, sun hallakashi yana da shekaru 58 daidai a duniya watanni 2 bayan yayi ritaya daga aikin soji.

Hakika arewa tayi babban rashin jan gwarzo wanda ya kammala aikin soji lafiya.

Anyi mana asarar da ba zamu iya cike gurbinta ba, irinsa ne suka dace da su shugabanci al'umma a babin siyasa saboda kishinsa da kuma gaskiyarsa.

Muna rokon Babban Sarki Allah da Ya amshi shahadar Janar Idris Alkali

Allah Ka yafe masa kura-kurensa sannan Ka saka masa da Aljannar Firdausi Amin.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel