Wata mata ta bukaci kotu ta raba aurenta da mijinta, saboda ko kadan bata kaunar mijin nata

Wata mata ta bukaci kotu ta raba aurenta da mijinta, saboda ko kadan bata kaunar mijin nata

- Rashin haihuwa ya tilasta wata mata garzayawa kotu ta na rokon Alkali ya taimaka ya raba aurenta da mijinta bayan sun shafe shekaru goma suna tare

- Sai dai kuma mijin matar ya ce shi tsakani da Allah ya na kaunar matarshi

A yau Alhamis dinnan ne 11 ga watan Afrilu, wata matar aure mai suna Aishatu Mohammed, ta kai karar mijinta kotun shari'ar musulunci dake garin Minna babban birnin jihar Niger, inda ta ke bayyana cewa bata son mijin nata ko kadan yanzu, kuma ta na rokon kotu ta raba auren da ke tsakaninta da mijin nata.

Aisha ta bayyanawa kotu cewar gaskiya bata kaunar mijinta, mai suna Tanimu wanda suka shafe shekaru 10 suna tare babu haihuwa.

Wata mata ta bukaci kotu ta raba aurenta da mijinta, saboda ko kadan bata kaunar mijin nata
Wata mata ta bukaci kotu ta raba aurenta da mijinta, saboda ko kadan bata kaunar mijin nata
Asali: Twitter

"Mijina yana kula dani ta kowanne fanni na zaman aure, wasu lokutan ma yana kula dani fiye da yadda nake tunani, amma gaskiya bana kaunarshi yanzu."

"Saboda haka ina rokon wannan kotu mai adalci da ta raba aurenmu."

Sai dai shi kuma Tanimu, ya ce har yanzu yana son matar tashi, kuma bai son abinda zai sa su rabu.

KU KARANTA: Dangote ya bayyanawa matasa hanyar da za su zama kamar shi

Ya roki kotu ta bashi lokaci ya yi kokari ya shawo kan matarshi, ko za ta canja ra'ayi.

Alkalin kotun, mai shari'a Ahmed Bima, ya shawarci ma'auratan su yi shawara a junansu, inda ya kara da cewa aure dan hakuri ne, sannan kuma yana bukatar fahimtar juna.

Alkalin kotun ya daga karar ma'auratan har zuwa ranar 29 ga watan Afrilun nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng