Ba Hutu: Kotu Ta Raba Auren Wani Ɗan Acaɓa Da Matarsa Saboda Jarabar Ta Da Saduwa a Kowane Rana

Ba Hutu: Kotu Ta Raba Auren Wani Ɗan Acaɓa Da Matarsa Saboda Jarabar Ta Da Saduwa a Kowane Rana

  • Wata kotu da ke Igando a Jihar Legas ta raba auren Taofeek Muritala da Jelilat Muritala sakamakon yadda kullum suke rikici da kuma rashin soyayya tsakaninsu
  • Mai karar, Muritala ya gabatar wa da kotu kara a watan Disamban 2021 yana neman a raba aurensu mai shekaru 10 da matarsa sakamakon taurin kanta
  • A bangaren matar, Jelilat Muritala, ta ce suna samun matsala da mijinta ne saboda kwanciyar aure, yana da bala’in jaraba don kullum sai ya nemeta

Jihar Legas - A ranar Talata wata kotu da ke Igando ta raba auren Toafeek Muritala da Jelilat Muritala saboda yawan fadace-fadace da rashin soyayya, NAN ta ruwaito.

Mai karar, Muritala, wanda mazaunin gida mai lamba 11, Muritala Taofeek St., White Sanda area da ke Isheri a Jihar Legas, ya kai kara kotu a ranar 2 ga watan Disamban 2021 yana neman a raba aurensu mai shekaru 10 da matarsa.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

Kotu ta raba auren wani dan acaba akan yadda ya dami matarsa da kwanciyar aure kullum
Kotu ta raba auren dan acaba saboda matarsa ta gaza biya masa bukata na kwanciyar aure. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Facebook

Ya zargi matarsa da rashin ji da taurin kai tare da rashin kulawa da yaransa. Kamar yadda ya shaida wa kotu:

“Mun fara fuskantar matsaloli tun a shekarar 2002 ne lokacin ina aikin acaba a lokacin ta haihu. Na kasance ina bata N100 kullum. Daga baya na kasa ci gaba da biyanta kudin saboda akwai kudaden da nake kai wa mai babur din da nake tukawa.”

A cewarsa har cin kwalarsa take yi

Daily Nigerian ta bayyana yadda ya ci gaba da cewa:

“Akwai ranar da ta yi lissafi inda tace wai N900 take bi na. A ranar ta ci kwalata tana ta bala’i akan cewa sai na biyata kudin ko kuma ta hana ni fita. Har sai da makwabta suka shiga tsakaninmu, har tana yaga kayana.

Kara karanta wannan

Halin bera: Yadda sabon ma'aikaci ya tsere da cinikin rana guda na gidan burodi

“Akan karamin fada sai ta yi yaji. Bata girmama mahaifiyata. Tana yawan fada da ita, har ta kai ga na dakatar da mahaifiyata daga zuwa gidan.”

Ya ci gaba da cewa bata kulawa da yaransu. Tana yin duk abinda ta ga dama. Idan fada ya hadasu har da wuka da fasasshiyar kwalba take kai mishi farmaki. Hakan yasa yake so a raba aurensu.

Naci wurin kwanciyar aure ya janyo fadarsmu, Jelilat

A bangaren Jelilat Muritala, ta ce fadan nasu yana da nasaba da kwanciyar aure. Ta ce a ko wacce rana sai ya nemi su kwanta har ta kai ga ta gaji.

Kamar yadda ta shaida, mahaifiyarsa ba ta kaunarta, duk abinda ta yi sai ta kushe amma tana da alaka mai kyau da duk sauran ‘yan uwansa.

Alkalin ya shimfida wa Muritala wasu dokoki

Alkalin kotun, Mr Koledoye Adeniyi, bayan sauraron korafin ko wanne bangare ya amince da raba auren.

Kara karanta wannan

Manyan jaruman kannywood maza 4 da suka shafe sama da shekaru 20 suna fim kuma ake yi da su har yau

Ya ce ba daidai bane mace ta hana mijinta kanta yayin da ya ke bukatarta ko da kuwa kullum ne. Kuma kin amincewa da mijin zai iya janyo ya fara neman matan waje.

Ganin wadannan hujjojin ne alkalin ya raba auren inda ya ce Muritala ya biya Jelilat N200,000 a matsayin tallafi, sannan ya bata N150,000 don ta nemi wurin zama.

Ya kuma nemi Muritala ya dinga kulawa da yaransu har su girma. Kuma duk wanda ya ki bin dokar kotu zai yi watanni 6 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara

Ba zan iya ba: Jarabar mijina ta yi yawa, yana so ya kashe ni da saduwa, Matar aure ga kotu

A wani labarin, wata matar aure mai 'ya'ya uku, Olamide Lawal, a ranar Juma'a ta roki kotun Kwastamare da ke zamansa a Mapo, Ibadan, ya raba aure tsakaninta da mijinta, Saheed Lawal, saboda yana jarabar ta da yawan saduwa, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Amurka ta amince Buhari ya kashe $1bn domin shigo da wasu jiragen yaki

A karar da ta shigar, Olamide wacce ke zaune a Ibadan ta kuma yi ikirarin cewa mijinta ya saba shan giya ya yi tatil yana maye, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel