Aminu Sanusi ya kama aiki gadangadan a matsayin dan sanda (hotuna)
Aminu Sanusi, dan tsohon gwamnan babban bankin kasa kuma sarkin Kano a yanzu, mai martaba Muhammad Sanusi Lamido ya kama aikinsa na dan sanda gadan-gadan.
Matashin mai shekaru 26 wanda ya kasance da na farko a wajen sarkin ya kasance daga cikin sababbin yan sandan da gwamnatin tarayya ta diba kwanan nan.
Ya sha ruwan yabo daga jamiár hulda da jama’a na sashin sa Misis Opetodola Badmos a ranarsa ta farko a matsayin jami’in dan sanda a shafinta na Instagram.
Idan za a tuna kakan matashin, marigayi, Sarki Ado Bayero ya kasance jami’in dan sanda kafin ya koma aikin diflomasiyya, daga bisani kuma ya zamo sarkin Kano.
KU KARANTA KUMA: Sai mun rungumi gaskiya da nagarta sannan za mu cimma nasara a matsayin kasa - Osinbajo
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng