Wani mutum yayi alkawarin bawa duk wani wanda yayi rijistar zabe naira 1000

Wani mutum yayi alkawarin bawa duk wani wanda yayi rijistar zabe naira 1000

- A kudu maso gabas ake so mutane suyi rajistar

- An gano mutanen yankin sune mafi karancin masu rajista a shiyyoyin Najeriya

- INEC ta saki jaddawalin masu rajista shiyya shiyya

Wani mutum yayi alkawarin bawa duk wani wanda yayi rijistar zabe naira 1000
Wani mutum yayi alkawarin bawa duk wani wanda yayi rijistar zabe naira 1000

A kokarinsa na kara wa jama'arsa da yankinsa tagomashin siyasa, wani mutum daga kabilar Ibo, ya sha alwashin rabok kudi, Naira dubu-dubu, ga duk wani wanda ya garzaya yayi rajista a ofishin hukumar INEC, daga shiyyar kudu maso gabas.

Su dai kabilun Ibo, wadanda suke ganin kamar ana zaluntar su, kuma ana musu wariya, tun zamanin mulkin basasa, har yanzu, basu yo siyasar tsakiya ba, inda kullum basu iya hada kai su dunkula kuri'unsu wuri guda.

A wannan karon, ga alama sun farka, ganin yadda suke ta kayya-kayya a yanar gizo kan ko su balle ko su bata wa shugaba Buhari suna, musamman ganin ya kayar musu da dan-gida Ebele Jonathan.

DUBA WANNAN: Da alamun hukumar NEDC zata kawo sauyi ga mutanen Arewa maso gabas

A jaddawalin shiyyoyin Najeriya dai da aka fitar, yankin kudu maso gaban din na Igbo, shine mafi kankantar jama'a wadanda suka yi rajista domin shiga zabuka su kada quri'u a badi.

Shiyyoyin, sun hada da arewa ta tsakiya, ta gabas da ta yamma, kudu maso kudu, maso yamma ta Yarabawa da ta gabas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng