Magani a gonar yaro: Amfanin ganyen rogo guda 6 a jikin mutum da ya kamata kowa ya sani

Magani a gonar yaro: Amfanin ganyen rogo guda 6 a jikin mutum da ya kamata kowa ya sani

- Ganyen rogo ana iya sarrafashi ta hanya daban-daban

- Ba maganin yunwa kadai yake ba, yana da wasu amfani ga jikin dan Adam

- Hakan na faruwa ne sakamakon sinadaren da yake kunshe a rogo, sassakenshi da ganyenshi

Ganyen rogo ana iya sarrafashi zuwa abinci kala-kala. Za a iya miya dashi tamkar kayan lambu. Ganyen ya kunshi isassun sinadaran Vitamin A da B1, fiber, protein da amino acid, wadanda suke taka rawar gani wajen karin lafiya ga jikin dan Adam.

Ga kadan daga cikin amfanin ganyen rogo a jikin dan Adam.

1.Ganyen rogo na sa mutum ya so cin abinci

A gargajiyance, sassaken rogo, asalin rogon da ganyenshi ana amfani dasu wajen yin magani. A kan hada ganyenshi da citta ko tafarnuwa don samun sanya wa mara lafiya bukatar abinci. Ana shan shi ne da safe kafin a ci komai.

2. Yana kara karfin jiki

Saboda sinadarin Protein da amino acid da ke kunshe a ganyen rogo, yana taimakawa wajen ba wa jiki karfin da yake bukata.

3. Yana maganin ciwon kafa

Don yin wannan maganin, ana dafa ganyen rogo ne tare da citta da kuma ciyawa. Bayan an tace su, ana iya sha sau biyu a rana; safe da rana.

KU KARANTA: Hotuna: A karon farko an kirkiri jirgin kasa da yafi jirgin sama gudu a kasar China

4. Ganyen rogo na bunkasa farfadowa da maye gurbin kwayoyin halitta a jikin mutum

Saboda sinadarin amino acid da ke kunshe a ganyen rogo, yana sa mayewar gurbin lalatattun kwayoyin halitta.

5. Yana maganin Zazzabi da ciwon kai

Ganyen rogo na maganin zazzabi da ciwon kai. Wajen hada wannan maganin, ana dafa sassaken rogo ne tare da ganyenshi. Bayan ya huce sai a dinga sha.

6. Yana kara garkuwa ga jikin dan Adam

Saboda yawan sinadarin folate da Vitamin C, ganyen rogo na kara garkuwa ga jikin dan Adam tare da karfin kashi. Sinadarin Vitamin C din na taimakawa wajen yakar kwayoyin cuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng