Yadda mu ka tsira a harin da ‘Yan bindiga su ka kawo inji ragowar Dalibai, Malaman GSSS Kagara

Yadda mu ka tsira a harin da ‘Yan bindiga su ka kawo inji ragowar Dalibai, Malaman GSSS Kagara

- Wadanda su ka sha a hannun ‘Yan bindiga a Kagara sun fito sun yi magana

- Akwai dalibai da ma’aikatan makarantar GSSS Kagara da su ka iya tserewa

- Wani Bawan Allah da ke garin ya ce har yanzu bai san inda iyalansa su ke ba

Wasu ragowar dalibai da ma’aikatan makarantar sakandaren kimiyya ta kwana ta Kagara, sun bada labarin mugun harin da ‘yan bindiga su ka kawo masu.

Wadannan Bayin Allah sun taki sa’a, domin kuwa ‘yan bindigan ba su yi nasarar cafke su ba, sun shaida wa ‘yan jarida yadda su ka kubuta daga wannan hari.

Wani dalibin makarantar mai suna Ndako, ya fada wa jaridar The Nation cewa da ya ga ‘yan bindigan, sai ya tsere cikin daji, su ka yi ta harbi, ya na gudu.

“Na yi sa’a, na ci karo da wani gida, sai na boye a bayan shi. Wasu dalibai uku sun zo sun same ni, mu ka labe a nan har sai zuwa da safe, sannan mu ka fito.”

Yadda mu ka tsira a harin da ‘Yan bindiga su ka kawo – Ragowar Dalibai, Malaman GSSS Kagara
Garin Kagara Hoto: thenationonlineng.net
Source: UGC

KU KARANTA: Kalaman Ministan tsaro a Neja sun jawo ana kiran a tsige shi

Aliyu Isah wanda malami ne a makarantar da wannan abu ya faru, ya ce ya yi mamaki da ya yi rai.

“Na tsere zuwa fili, su kuma su ka yi ta harbi na. Ba a tsaye na rika gudu ba, ina ta zillo domin in kauce wa harsashensu. Na yi ta gudu har na ga wani gida.”

Malam Isah ya ce a wannan gida ya boye zuwa karfe 2:00 na tsakar dare, a wannan lokaci ne ‘yan bindigan su ka tattara mutanen da su ka kama, su ka tafi.

Ndako da Isah sun fada wa ‘yan jarida cewa ‘yan bindigan sun shigo makarantar sakandaren ne dauke da kayan sojoji, su ka auka wa dakin kwanan dalibai.

KU KARANTA: Abin da Shugabannin sojoji su ka fada da su ka bayyana gaban Majalisa

Wani mazaunin Kagara, Khamis Tahir, ya ce bai san inda ‘diyarsa da mutane shida daga cikin iyalinsa su ke ba, amma ya ce surukinsa ya iya samu ya tsere.

Akwai sauran yara da jama’an da Allah ya yi wa gyadar doguwa da Miyagu su ka shiga Kagara. Wani ya ce gudu na yi ta yi, ina cikin gudu sai na iske wani gida, na boye.”

A baya kun samu labari cewa majalisar dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da dauke mutane da aka yi a makarantar GSSS Kagara a ranar Laraba, 17 ga watan Fubrairu, 2021.

Shugaban majalisar dinkin Duniya, Antonio Guterres ya fitar da jawabi ya ce ba za ta yiwu a rika zuwa makaranta ana sace Bayon Allah ba, don haka ya yi kira a ceto su.

Haka zalika kungiyar UNICEF ta fitar da jawabi da kalmomi masu tsauri, ta soki wannan danyen aiki.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel