Tinubu Ya Yi Alkawarin Biyan Matasan N-Power Basukan Watanni 8 Nan Kusa

Tinubu Ya Yi Alkawarin Biyan Matasan N-Power Basukan Watanni 8 Nan Kusa

  • Yayin masu cin gajiyar N-Power ke korafin basukan da su ke bi, kakarsu ta yanke saka a yanzu
  • Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin biyan matasan basukan da su ke bi na tsawon watanni tara
  • Manajan shirin, Akindele Egbuwalo shi ya bayyana haka inda ya ce sun samu wasu kudade don biyan basukan

FCT, Abuja – Manajan shirin N-Power a Najeriya, Akindele Egbuwalo ya bayyana cewa sun shirya tsaf don biyan masu cin gajiyar bashin da su ke bi na watanni takwas.

Egbuwalo ya bayyana haka ne a yau Asabar 14 ga watan Oktoba a cikin wata sanarwa inda ya ce sun samu wasu kudade wanda za su yi amfani da su, Legit ta tattaro.

Tinubu ya yi alkawarin biyan basukan matasan N-Power
Tinubu ya yi martani kan basukan matasan N-Power. Hoto: @officialABAT, @edu_betta.
Asali: Twitter

Meye gwamnatin Tinubu ke cewa kan shirin N-Power?

Yayin da ya ke magana da wakilan masu cin gajiyar N-Power, Egbuwalo ya ba da tabbacin cewa za a fara biyan basukan nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Basuka: Matasa Masu Cin Gajiyar N-Power Sun Koka Da Rusa Shirin, Sun Tura Muhimmin Sako Ga Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Labari mai dadi shi ne an samu wasu kudade kuma za mu fara biya nan ba da jimawa ba.
“Zamu fara biyan basuka ne na masu cin gajiyar N-Power da ke bin gwamnati bashi na watanni takwas nan kusa.”

Ya kara da cewa Minista Betta Edu ta himmatu wurin tabbatar da kawo gyara a cikin shirin da sauran shirye-shirye da su ka shafi ma’aikatar.

Ya karawa matasan kwarin gwiwa da su kara hakuri yayin da su ke ci gaba da kawo gyara a shirin don inganta shi tare da diban miliyoyin ‘yan kasar, The Nation ta tattaro.

Yaushe aka kirkiri shirin N-Power?

Egbuwalo ya ba da tabbacin cewa Shugaba Tinubu ya himmatu wurin dakile talauci a kasar inda ya ce kuma ya kama hanyar cika wannan alkawari.

Tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ce ta kirkiri shirin N-Power inda ake biyan matasa Naira dubu 30 ko wane wata wanda ya rage yawan talauci a tsakanin matasa.

Kara karanta wannan

Wike Ya Kafa Doka Kan 'Yan Bola Jari Da Masu Baban Bola Shiga Yankunan Abuja, Ya Fadi Matakin Gaba

Daga bisani gwamnatin Bola Tinubu ta dakatar da shirin inda ta ce za ta yi bincike kan zargin badakalar kudade a shirin.

Matasan N-Power sun roki Tinubu ya biya su basukan wata 9

A wani labarin, matasa masu cin gajiyar N-Power sun roki Shugaba Tinubu da ya biya su bashin watanni tara da su ke bin gwamnati.

Shugabannin matasan a jihar Gombe, sun bukaci gwamnatin da ta tausaya musu ganin halin matsin da ake ciki a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel