Hukumar IMF Ta Bai Wa Najeriya da Sauran Kasashen Afirka Sharadin Yafe Musu Basuka

Hukumar IMF Ta Bai Wa Najeriya da Sauran Kasashen Afirka Sharadin Yafe Musu Basuka

  • Hukumar IMF ta yi biris da bukatar Najeriya da sauran kasashen Nahiyar Afirka kan yafe musu basukan da su ka ci
  • Ta ce kasashen da ke bukatar yafiya na bashin su yi zama da kasashen da su ka ba su ta yadda za su sami mafita
  • Wakilin hukumar IMF a Nahiyar Afirka, Abebe Salessie ya bukaci kasashen Nahiyar Afirka da su rage tashin farashin kaya a kasashensu

FCT, Abuja Hukumar Ba da Lamuni ta IMF ta karyata cewa za ta yafewa Najeriya da Ghana da sauran kasashe dukkan basukan da ta ke bi.

Darakan yankin Afirka na IMF, Abebe Selassie ya ce kaso 50 na basukan kasashen na gida ne wanda zai yi wahalar yafiya, Legit ta tattaro.

Hukumar IMF ta gindaya sharuda na yafe wa Najeriya basuka da sauran kasashe
Hukumar IMF Ta Bai Wa Najeriya Da Sauran Kasashen Sharuda Biyan Bashi. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Meye IMF ta ke cewa kan basukan Najeriya?

Kara karanta wannan

Isra'ila v Falasdinu: Shahararren Malamin Addini Ya Bayyana Matsayarsu Akan Wannan Rikici, Ya Tura Sako

Ya ce babu yadda za a yi a yafe basukan haka nan dole akwai bukatar tattaunawa da kasashen da su ka ba su basukan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar kula da basuka a Najeriya, DMO ta ce basukan da ake bin kasar ya kai Naira tiriliyan 87 a watan Yuni na 2023.

The Nation ta ruwaito Selassie na cewa babu wani ci gaba da aka samu a bangaren zuba jari masu zaman kansu inda ya ce ana sa rana samun karuwa a Nahiyar zuwa 2024.

A shekarar 2022, hukumar IMF ta gargadi Najeriya da sauran kasashen Afirka masu tasowa daga karbar lamuni daga kasar China saboda tsanani da ke cikin basukan.

Wane roko Najeriya da sauran kasashe ke yi wa IMF?

Najeriya da sauran kasashen Nahiyar Afrika na rokon yadda za a yafe musu kudaden da ake binsu.

Kara karanta wannan

Najeriya ta Samu Dama Bayan Karya Tarihin Tsawon Shekara 60 a Bankin Duniya

Kasashen G24 sun mika kokon bara ga IMF da kuma Bankin Duniya yayin da ake wata ganawa a birnin Marakesh da ke kasar Morocco.

Kasashen na G24 sun koka kan yadda basukan ke kara yawa a kansu inda su ka ce su na bukatar taimako.

Ministan kudade da tattalin arziki a Najeriya, Wale Edun ya ce G24 sun nemi da a kawo karshen basukan don kawo dauki bayan wucewar annobar Korona.

NNPC na bin Gwamnatin Najeriya Naira tiriliyan 7

A wani labarin, kamfanin mai na NNPC ya bayyana cewa ya na bin Gwamnatin Najeriya Naira tiriliyan 7.3 na tallafin mai.

NNPC ya ce kafin cire tallafin mai a watan Mayu da Tinubu ya yi, ya na kashe Naira biliyan 400 a ko wane wata don shigo da man fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel