Yan Siyasa 3 Da Suka Shafe Sama Da Shekaru 8 a Kan Kujerar Gwamna a Najeriya

Yan Siyasa 3 Da Suka Shafe Sama Da Shekaru 8 a Kan Kujerar Gwamna a Najeriya

  • Wasu gwamnoni sun yi fiye da shekaru takwas da dokar kasa ta kayyade a matsayin wa’adin zababbun masu mulki
  • Daga cikin ‘yan siyasar da hakan ta faru da su akwai Ibrahim Gaidam wanda ya yi mulkinsa tun daga 2009 har zuwa 2019
  • Jolly Nyame da Bukar Abba Ibrahim sun zama gwamnoni a lokacin mulkin soja, da aka dawo farar hula su ka sake mulki

Abuja - Daga lokacin da aka fara siyasar farar hula a tarihi zuwa yanzu, an yi wasu gwamnonin da su ka yi sa’a, aka rantsar da su har sau uku.

Bayan an dawo farar hula a mulkin sojan Janar Ibrahim Badamasi Babangida a 1991, ‘yan siyasa sun shiga takara a karkashin jam’iyyun SDP da NRC.

Wasu daga cikin wadanda su ka yi mulki a wancan lokaci kafin zuwan Janar Sani Abacha, sun sake yin takara a jihohinsu da sojoji su ka bar mulki.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga, Sun Ceto Sama da Mutum 170 da Aka Sace a Jihar Arewa

Gwamna
Wadanda su ka yi Gwamna sau uku Hoto: dailypost.ng, independent.ng, www.naijanews.com
Asali: UGC

Gwamna ya mutu, mataimaki ya hau

A dalilin rasuwar shugaba, wasu mataimakan su kan yi sa’a a rantsar da su a kan kujera, daga baya kuma sai su nemi takara da kan su, su ci zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit ta kawo jerin ‘yan siyasar da su ka yi sama da shekaru takwas a kujerar gwamna.

1. Gwamna Jolly Nyame

Rabaren Jolly Nyame ya yi takarar Gwamna a Taraba a 1992 kuma ya yi nasarar lashe zabe, sai dai ba a dade ba, sojoji su ka sake komawa mulki.

A 1999 har wa yau, Nyame ya tsaya neman Gwamna a inuwar PDP ya sake samun nasara kamar yadda aka yi a 2007 da ya zarce a karo na biyu a jere.

2. Gwamna Bukar Abba Ibrahim

Jim kadan da kirkirar Yobe a matsayin jiha daga tsohuwar Borno, Bukar Abba Ibrahim ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar SDP, ya yi mulki a 1992.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sace Malamin Musulunci Yayin Da Su Ke Raka Gawa Makabarta, Bayanai Sun Fito

Bayan ya bar ofis a Nuwamban 1993, sai Bukar Abba ya sake shiga takara sau biyu a jere a APP da ANPP, ya bar karagar mulki ne a watan Mayun 2007.

3. Gwamna Ibrahim Gaidam

A jihar Yoben ne kuma aka rantsar da Ibrahim Gaidam a matsayin gwamna a Junairun 2009 a sakamakon rasuwar Mai girma Mamman B. Ali.

Da aka zo zaben 2011 sai ANPP ta sake tsaida Ibrahim Gaidam, haka aka yi a 2015 wanda hakan ya ba shi damar zama gwamna a karo na uku a jere.

Za a karbe kujerar Gwamnan Kano?

Kwanaki kun ji labari Abba Kabir Yusuf ya garzaya kotu domin ya cigaba zama a kan kujerar Gwamna a Jihar Kano bayan kotun zabe ta tunbuke shi.

Wannan karo, Wole Olanipekun SAN wanda ya kware a shari’ar zabe ne sai kare Abba Gida Gida a kan APC da Nasiru Gawuna da aka ba nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel