Shin Da Gaske An Sanya Wa Ministar Tinubu Guba? Gaskiya Ta Bayyana

Shin Da Gaske An Sanya Wa Ministar Tinubu Guba? Gaskiya Ta Bayyana

  • Ma'aikatar wuraren tarihi da buɗe ido ta musanta rahoton da ke yawo cewa minista, Lola Ade-John, ta ci guba an kwantar da ita a asibiti
  • Mai magana da yawun ma'aikatar ta ce rahoton ba gaskiya bane amma ministar na fama da zazzabin cizon sauro wanda a yanzu ta samu sauƙi
  • Raɗe-raɗi ya yaɗu a kafafen sada zumunta cewa ministar na kwance a Asibitin Abuja bisa zargin an ba ta guba

FCT Abuja - Ma'aikatar kula da wuraren tarihi da buɗe ido ta musanta rahoton da ke yawo a soshiyal midiya cewa ministar wuraren buɗe ido, Lola Ade-John, ta ci guba kuma an garzaya da ita Asibiti.

Yayin da jaridar Vanguard ta tuntuɓi ma'aikatar, mataimakiyar daraktan yaɗa labarai, Emem Mariam Ofiong, ta ƙaryata rahoton cewa minista ta sha ko ta ci guba.

Kara karanta wannan

An zo wajen: An nemi Tinubu ya fadi nawa tara bayan cire tallafin mai, kuma nawa ya kashe

Ministar wuraren tarihi da buɗe ido, Lola Ade-John.
Shin Da Gaske An Sanya Wa Ministar Tinubu Guba? Gaskiya Ta Bayyana Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Menene gaskiyar abin da ya faru da Ministar?

Amma ta tabbatar da cewa zazzaɓin cizon sauro ya lulluɓe Ministar wuraren bude ido da tarihi kuma tuni aka bata kulawar da ta dace har ta samu sauƙi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamanta, Emem Mariam Ofiong ta ce:

"Ba gaskiya ba ne cewa guba aka bai wa Ministar, zazzabin cizon sauro ne kawai ga kwantar da ita, kuma an mata magani yanzu ta dawo daidai."

Idan dai baku manta ba, wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna cewa ministar harkokin yawon bude ido, Lola Ade-John, na kwance a asibiti a babban birnin tarayya Abuja.

Rahoton ya yi ikirarin cewa an garzaya da ita Asibiti ne bisa zargin ta ci guba, tana kwance a FMC da ke Jabi a Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Auren Sadiya Haruna Da G-Fresh Ya Shiga Tangal-Tangal, Rigima Ta Kai Gaban Alkali

Sai dai a yanzu, ma'aikatar da take jagoranta ta musanta wannan rahoto da cewa ba gaskiya bane, zazzaɓin cizon sauro ne kuma ta samu kulawar da ya kamata.

Misis Lola Ade-John, ita ce Ministar wuraren buɗe ido ta farko bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya raba ma'aikatar yaɗa labarai da al'adu a Najeriya.

Yajin Aiki: Kungiyar Kwadago Ta Kaurace Wa Taron da Gwamnatin Tinubu Ta Shirya

Legit Hausa ta rahoto cewa Wakilan ƙungiyoyin NLC da TUC sun yi watsi da taron da gwamnatin tarayya ta shirya a fadar shugaban ƙasa ranar Jumu'a.

Ministan kwadago da shugaban ma'aikatan Villa sun kammala shirin taron amma shiru shugabannin ƙungiyoyin suka ƙi zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel