Mutumin da Ya Shafe Shekaru 20 a Kasar Kanada Ya Yi Danasani, Ya Dawo Najeriya Don Ci Gaba da Aiki

Mutumin da Ya Shafe Shekaru 20 a Kasar Kanada Ya Yi Danasani, Ya Dawo Najeriya Don Ci Gaba da Aiki

  • Wani mutumin da ya yi hijira zuwa kasar Kanada ya ce ya fi samun kudi a kasar da yake a baya kafin ya koma Kanada
  • Duk da zama a Kanada na shekaru 20, ya ce gidaje biyu ne kadai ya gina a tsawon zamansa a kasar ta waje
  • Mutane da yawa sun yi martani a kai, inda suka rabu wajen bayyana ra'ayi da abin da suka fahimta a labarin nasa

Wani mutum mai matsakaicin shekaru ya bayyana dana-sanin tattara kayansa tare da barin gida, inda ya koma rayuwa a Kanada.

Mutumin ya ce, da zamansa ya yi a kasarsa da yanzu ya samu arziki da kayan duniya fiye da na rayuwarsa a Kanada.

Ya bayyana cewa, dole yanzu haka ya koma kasarsa tare da ci gaba da aiki duk da shafe shekaru sama da 20 a kasar ta Kanada.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Elon Musk zai kawo wani sabon tsarin da ba a taba ba a Twitter

Yadda wani ya rayu a Kanada ya dawo babu ko kobo
Mutumin da ya samu kudi kadan a Kanada cikin shekaru 20 | Hoto; @polleksandra
Asali: TikTok

Ya kuma kara da cewa, ya yi amfani da kudaden da ya tara a kasar Kanada wajen sayen gidaje biyu kacal.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun yi mamaki, sun kuma bayyana ra'ayoyinsu da bayanai masu kama da shawari.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

A bidiyon da @polleksandra. ya yada, mun tattaro muku kadan daga abin da jama'ar kafar sadaz umunta ke cewa kamar haka:

brrrrr:

"Daga karshe dai mutane sun fara gani."

philpain656:

"Ka tara kudi a Kanada sannan ka dawo wata kasa."

Daveysclavey:

"Ya mutumin da bai da gida kuma a ce ya dawo."

Suleman:

"Watakila zamansa da ya yi a Kanada na shekaru 20 ne suka koya masa yadda zai samu kudin ciki shekaru bakwai."

David Turcotte:

"Akwai kitimurmura da yawa a cikin labarin nan. Meye ya yi a Caribbean har ya samu kudi da yawa a shekaru 7?

Kara karanta wannan

Yadda Matasa Suka Babbaka Wani Mai Satar Yara a Arewacin Najeriya, Sun Ceto Mata 2 Da Ya Sace

Ta zama mai jiran shago bayan zama a kasar waje

A wani labarin, wata matashiyar budurwa ta je shafin soshiyal midiya don bayyana yadda tayi tawakkali duk da cewar rayuwa ta juya mata baya.

A cikin wani bidiyon TikTok, ta bayyana cewa bayan ta shafe shekaru uku a kasar Larabawa, ta dawo gida ta kama sana’ar bakin hanya, yanzu tana jiran shagon caca ne.

A yayin daukar bidiyon, an gano matar tana aiki a na’urar buga caca yayin da take taka rawa. Ta bayyana cewa duk da halin da take ciki, tana godiya ga Allah da ya barta da ranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel