“Albashina Na Farko a Canada”: Matashi Da Ya Koma Turai Da Zama Ya Siya Mota Da Albashinsa Na Farko

“Albashina Na Farko a Canada”: Matashi Da Ya Koma Turai Da Zama Ya Siya Mota Da Albashinsa Na Farko

  • Wani dan Najeriya da ke zaune a kasar Canada a yanzu ya yi amfani da kudin da ya karba a matsayin albashi wajen siyan mota kirar Honda Civic
  • Mutumin mai suna Abwire wanda ya cika da farin ciki, ya ce ya zuba albashinsa na farko wajen siyan farar Honda sannan ya wallafa bidiyon motar a TikTok
  • Bayan bidiyon ya bayyana, mabiyansa da dama sun shiga sahun masu aika masa da sakonni na taya murna

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani dan Najeriya da ke zaune a kasar Canada ya siyawa kansa sabuwar mota kirar Honda Civic, kuma ya garzaya dandalin TikTok don yin murna.

Mai motar, Abwire, ya wallafa bidiyon motar a dandalinsa na TikTok, kuma abokai da mabiyansa sun taya shi murna.

Matashi ya siya mota da albashinsa na farko
“Albashina Na Farko a Canada”: Matashi Da Ya Koma Turai Da Zama Ya Siya Mota Da Albashinsa Na Farko Hoto: @abwire1.
Asali: TikTok

Abwire ya bayyanawa mabiyansa cewa kudin da ya yi amfani da shi wajen siyan motar ya kasance albashinsa na farko a kasar Canada.

Kara karanta wannan

Wani Mutum Ya Sha Dauri Bayan Fadawa Fasto Laifin Da Ya Taba Tafkawa a Coci a Baya

Ya ce wannan shine biyan farko da aka yi masa a matsayin mazaunin Canada, kuma ya yi amfani da shi wajen gwangwaje kansa da farar mota kirar Honda Civic.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dan Najeriya mazaunin Canada ya siya mota da albashinsa na farko

Bidiyon ya nuno yadda Abwire ya cike da farin cikin mallakar mota a dan kankanin lokaci bayan ya koma Canada.

Abwire ya rubuta a jikin bidiyon:

"Albashina na farko a Canada. Na siya motata ta farko. Ina taya kaina murna."

Wasu mutane da suka ga bidiyon sun taya shi murna inda suka garzaya sashin kwamet domin taya shi murna. Wasu kuma sun bukaci Abwire ya fada masu irin aikin da yake yi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Lee min Ho ya ce:

"Don Allah kada ka yi fushi wani aiki kake yi?"

Kara karanta wannan

“Aikin Nan Akwai Hatsari Sosai”: Mai POS Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Karbi Jabun N100K Daga Kwastoma, Bidiyon Ya Yadu

@TonyAmor ya ce:

"Na kasance a Canada tsawon makonni biyu yanzu. Ina tsananin neman kowani irin aiki dan uwa."

@Loftus 777 ya tambaya:

"Wai a wannan Canada da nake ciki."

Yan mata yan gida 3 sun zama matukan jirgin sama, hotonsu ya dauka hankali

A wani labari na daban, wasu yan mata yan Najeriya uku da suka fito daga jihar Ondo wadanda iyayensu daya sun zama matukan jirgin sama.

Wani mai amfani da Twitter Oluyemi Fasipe ne ya wallafa hoton yan matan kuma tuni ya yadu tare da haifar da martani masu dadi daga bangarori daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel