'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Fasto, Ɗiyarsa da Wani Mutum Daya a Kalaba

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Fasto, Ɗiyarsa da Wani Mutum Daya a Kalaba

  • 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Malamin addinin Kirista da ɗiyarsa da wani mutum ɗaya a Kalaba, jihar Kuros Riba
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun sace abin harinsu a jirgin ruwa da misalin ƙarfe 8 zuwa 9 na daren ranar Alhamis
  • Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar ya ce tuni jami'an tsaro suka mamaye yakin domin ceto malamin da sauran mutum 2

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Cross River - Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani Fitaccen Fasto na babbar Cocin da ake ji da ita a Kalaba, Rabaran Mike Obiora, da ɗiyarsa da ƙarin wani mutum ɗaya.

Malamin yana wa'azi ne a shahararriyar Coci wacce ake kira, "Word Alive Church" da ke layin Anating a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba.

Yan bindiga sun sace Fasto a Kalaba.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Fasto, Ɗiyarsa da Wani Mutum Daya a Kalaba Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Vanguard ta tattaro cewa an sace Malamin tare da ɗiyarsa mai suna, Shalom, da wani magidanci da bai jima da tarewa a sabon gidansa ba da misalin ƙarfe 8 zuwa 9 na daren Alhamis.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda 'Yan Bindiga Suka Kutsa 'Hostel' Uku Suka Sace Ɗalibai Mata a Jami'ar Tarayya Ta Gusau

Bayanai sun nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun zo da Jirgin ruwa, wanda suka yi amfani da shi wajen tafiya da waɗanda suka ɗauka bayan sun gama abinda ya kawo su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane matakin rundunar 'yan sanda ta ɗauka?

Yayin da aka tuntubi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Kuros Riba, SP Irene Ugbo, ya tabbatar da garkuwa da mutanen.

Ya ce dakarun 'yan sanda ba zasu huta ba har sai sun tabbatar da sun kubutar da Faston da sauran waɗanda aka sace tare da shi, jaridar Within Nigeria ta ruwaito.

Kakakin 'yan sandan ya ce:

"Mun samu rahoton abin da ya auku kuma tuni jami'an mu suka tsunduma aikin ceto jim kaɗan bayan samun kiran gaggawa, ba zamu yi ƙasa a guiwa ba kuma ba zamu huta ba har sai an gano su."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Sanda Sun Tono Gawar Fitaccen Mawakin Nan Da Ya Mutu, Bayanai Sun Fito

"Jami'an sashin dabaru sun kewaye yankin baki ɗaya tun jiya har yau da safe, ba zamu tsagaita ba har sai mun kwato su."

Yadda 'Yan Bindiga Suka Shiga Dakunan Kwanan Daliban Jami'ar Tarayya Gusau

A wani rahoton na daban Wasu dalibai sun bayyana hanyoyin da 'yan bindiga suka bi suka shiga ɗakunan kwanan ɗalibai a jami'ar tarayya ta Gusau.

A wani faifan bidiyo da ake yaɗawa, wani ɗalibi ya ce maharan sun shiga ta Tagogi da Silin suka kwashi dalibai da yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel