Yan Bindiga Sun Sace Malamin Addini Da Wasu Mutum 6 a Enugu

Yan Bindiga Sun Sace Malamin Addini Da Wasu Mutum 6 a Enugu

  • Wasu miyagun ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane sun sace Rev. Fr. M. Okide, limamin cocin Katolika ta Enugu
  • Ƴan bindigan sun sace malamin ne tare da wasu matafiya mutum shida suna tsaka da gudanar da tafiyarsu
  • Ƴan bindigan har sun kira waya suna neman a ba su kuɗin fansa naira miliyan 100 (N100m) kafin su sako limamin da sauran mutanen

Jihar Enugu - Ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wani limamin cocin Katolika, Rev. Fr. M. Okide na cocin Katolika ta Enugu da wasu matafiya mutum shida a Enugu.

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa, lamarin ya auku ne da yammacin ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba a kan hanyar Eke-Affa-Egede a ƙaramar hukumar Udi ta jihar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Fadar Mai Martaba Sarki, Sun Ƙone Mutum Ɗaya

Yan bindiga sun sace limamin cocin Katolika a Enugu
Yan bindiga sun sace malamin addini da wasu mutum 6 a Enugu Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Nawa ƴan bindigan suka nema a ba su?

An tattaro cewa tuni masu garkuwa da mutanen suka tuntubi ƴan uwan ​​wadanda lamarin ya shafa ta wayar tarho, inda suka bukaci a biya su naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa, kafin su sako limamin cocin da sauran wadanda suka yi garkuwa da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar NewTelegraph ta ce masu garkuwa da mutanen sun bar yaran mutanen da suka sace a cikin suna kuka kafin zuwan jami'an ƴan sanda waɗanda suka ɗauko su.

Har yanzu dai rundunar ƴan sandan jihar ba ta mayar da martani kan lamarin ba, amma tuni jami’an rundunar ƴan sanda ta Udi suka yi wa yankin ƙawanya da nufin ganin an sako limamin cocin Katolikan da sauran mutanen da aka sace.

Akwai matsalar tsaro a jihar Enugu

Hakazalika kwana ɗaya kafin aukuwar lamarin, wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne,.sun kashe wani mutum da aka fi sani da Sunday Nwa Ugwuja, a hanyar Edem-Nrobo-Ezikolo-Abbi a ƙaramar hukumar Uzo Uwani.

Kara karanta wannan

Jami'an Tsaro Sun Samu Nasarar Ceto Mutane Masu Yawa Da Aka Yi Garkuwa Da a Jihar Arewa

Sunday yana kan hanyarsa ne ta zuwa Nsukka lokacin da lamarin ya auku, inda aka tabbatar da mutuwarsa a asibitin Bishop Shanaham, Nsukka sakamakon zubar jini wanda ya wuce ƙima.

Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Fadar Basarake

A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun kai farmaki a fadar wani basarake a jihar Osun, a ranar Lahadi, 17 ga watan Satumban 2023.

Ƴan bindigan a yayin harin sun halaka wani mai neman gurbin shiga jami’a, Ibrahim Qudus, tare da kona gawarsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng