Rashin wutar lantarki ya hana jiragen sama tashi a filin jirgin sama na Lagas

Rashin wutar lantarki ya hana jiragen sama tashi a filin jirgin sama na Lagas

  • An samu cikas a wajen tashin jiragen sama a filin tashi da saukar jirage na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Lagas
  • Hakan ya kasance ne sakamakon daukewar wutar lantarki a filin jirgin saman a ranar Asabar
  • Hukumar FAAN ta baiwa fasinjojin da suka yi cirko-cirko saboda lamarin hakuri

Lagos - An samu daukewar wutar lantarki a filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Lagas, lamarin da ya kawo cikas a tashin jirage, yayin da daruruwan fasinjoji suka yi jugum-jugum.

An tattaro cewa daukewar wutar wanda ya afku a safiyar ranar Asabar, 2 ga watan Afrilu, ya hana jiragen sama tantance fasinjojinsu, lamarin da ya haddasa cunkoso a filin jirgin.

Rashin wutar lantarki ya hana jiragen sama tashi a filin jirgin sama na Lagas
Rashin wutar lantarki ya hana jiragen sama tashi a filin jirgin sama na Lagas Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa wutar lantarkin ta dauke ne sakamakon ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya a daren ranar Juma’a har zuwa wayewar garin Asabar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya soke taron 'Birthday' dinsa don nuna jimamin harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Ci gaban ya shafi jirage da dama domin ya wakana ne a daidai lokacin da yawancin jiragen waje ke sauka da tashi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Manajar filin jirgin saman, Victoria Shin-Aba, ta ce daya daga cikin hanyoyin samun wutar nasu ne ya samu matsala da misalin karfe 11:00 na daren Juma’a sakamakon ruwan sama, lamarin da ya sauke ainahin hanyar wutar.

Hukumar FAAN ta bayar da hakuri

Daily Nigerian ta rahoto cewa hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya (FAAN), a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta tabbatar da faruwar lamarin tare da baiwa fasinjoji da sauran masu amfani da filin jirgin saman suka fuskanci daukewar wutar na wucin gadi hakuri.

Mai magana da yawun hukumar ta FAAN, Faithful Hope-Ivbaze, a wata sanarwa da ya fitar, ya dora alhakin daukewar wutar kan ruwan sama.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Baya ga Azman, kamfanin jirgin Air Peace ya dakatar da aiki a Kaduna

2023: Yahaya Bello Ya Yi Alƙawarin Mayar Da Ƴan Najeriya Miliyan 20 Attajirai Idan Aka Zaɓe Shi Shugaban Ƙasa

A wani labari na daban, mun ji cewa a ranar Asabar, Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ta bayyana wa kowa shirinsa na son tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, The Cables ta rahoto.

Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a Eagles Square da ke Abuja inda ya ce zai dada daga inda shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya, ta hanyar mayar da ‘yan Najeriya miliyan 20 miloniyoyi zuwa shekarar 2030.

Kamar yadda ya shaida, gwamnatin Buhari tana da shirin tsamo ‘yan Najeriya miliyan 100 daga cikin fatara zuwa shekarar 2030.

Asali: Legit.ng

Online view pixel