Azarɓaɓin Hadimi Ya Jawo Abin Kunya a UAE, Gwamnati Tayi Magana Biyu a Gaban Kowa

Azarɓaɓin Hadimi Ya Jawo Abin Kunya a UAE, Gwamnati Tayi Magana Biyu a Gaban Kowa

  • Daga baya gwamnatin tarayya ta yi cikakken karin bayani game da yarjejeniyar da aka yi da kasar UAE
  • An fahimci gaskiyar matsayar da aka cin ma da Mohamed bin Zayed Al Nahyan ya zauna da Bola Tinubu
  • Ajuri Ngelale ya ce za a cigaba da ba mutanen Najeriya kuma jirage za su fara tashi, alhali ba haka ba ne

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A ranar Alhamis gwamnatin tarayya ta ce babu wani lokaci da aka tsaida domin jiragen sama su cigaba da jigilar daga Najeriya zuwa UAE.

Daily Trust ta kawo rahoto da ya tabbatar da cewa cigaba da aikin kamfanonin Emirates da Etihad ba zai zama da wuri kamar yadda aka fada ba.

Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya hadu da Shugaban kasar UAE, Sheik Mohamed bin Zayed Al Nahyan, matsayar tattaunawarsu ta jawo abin magana.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Ministar Tinubu da Kitsa Yadda Za a Tsige Shugaban Majalisar Tarayya

Bola Tinubu
Bola Tinubu a kasar UAE Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

UAE: Gaggawan gwamnatin tarayya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da farko an ji yadda Ajuri Ngelale ya fitar da jawabi, ya na mai cewa an ci ma yarjejeniya cewa jiragen saman kasar UAE za su dawo aiki a Najeriya.

Tun a lokacin da sanarwar ta fito daga fadar shugaban kasa, hukumomin UAE ba su uffan ba, hakan ya jawo shakku wanda daga baya ya zama abin sabani.

Jawabin da mahukuntan kasar Larabawan su ka fitar a karshe ya tabbatar da cewa a shirye Najeriya da UAE su ke shirin hada-kai domin dawo da alakarsu.

Saura kiris a gama magana da kasar UAE

A yayin da yake magana a wajen wani taron kasashen Afrika da aka yi a Abuja, ministan jiragen sama, Festus Keyamo, ya yi karin haske kan batun.

This Day ta ce Festus Keyamo ya nuna ana kokarin kammala abubuwan da su ka rage a yarjejeniyar, wasu su na ganin hakan bai nufin an lashe amai.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Babban Albishir Ga Yan Najeriya Kan Gwamnatin Tinubu, Ya Ce Romon Dadi Na Nan Tafe

Ministan ya ce kafin ya bar Abu Dhabi, ya hadu da kamfanin kamfanin jirgin Emirate, amma ya ce ba zai fadi lokacin da za su cigaba da aiki a kasar ba.

Ba za mu iya tsaida lokaci ba. Sake dawo da kamfanin jirgi ya cigaba da aiki bai nufin za a je ne kawai a dauko wani jirgi da ya ke ajiye.
Babu jirgin da ke ajiye ba ya aiki a ko ina, dole su canza tashin jiragensu sannan su cigaba da bin hanyoyin. Za su samu izini ne daga gida.

- Festus Keyamo SAN

Ma'aikata sun gigice da gwamnati ta fara binciken zargin satar da aka yi da sunan shirin noma, ana zargin an yi haka ne a lokacin Godwin Emefiele.

Ana rade-radin wani hadimin tsohon gwamnan CBN ya na da akawun sama 40 da ake wawurar kudi yayin da manoma su ka rika jiran taki da iri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel