Musulmai Sun Bukaci Gwamna Adeleke Ya Amince Da Shari'ar Musulunci a Jihar Osun

Musulmai Sun Bukaci Gwamna Adeleke Ya Amince Da Shari'ar Musulunci a Jihar Osun

  • Musulmai a jihar Osun sun buƙaci gwamnan jihar Ademola Adeleke da ya amince da shari'ar musulunci a jihar dake yankin Kudu maso Yamma
  • Ƙungiyar musulman jihar Osun (OSMC) ita ce ta yi wannan kiran ga gwamnan domin muhimmincin da shari'ar musuluncin take da shi
  • Shugaban ƙungiyar Alhaji Mustafa Olawuyi shi ne ya yi wannan kiran inda ya buƙaci gwamnan da ya ƙara yawan malaman Larabci a makarantun jihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Osun - Ƙungiyar musulman jihar Osun (OSMC) ta yi kira ga gwamnan jihar, Sanata Ademola Adeleke, da ya amince da shari'ar musulunci a jihar. 

Shugaban ƙungigar OSMC, Alhaji Mustafa Olawuyi, shi ne ya yi wannan kiran lokacin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1445 a birnin Osogbo, babban birnin jihar, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Tsohon Gwamna Zai Maye Gurbin Omisore a Kujerar Sakataren Jam'iyyar Na Kasa? Bayanai Sun Fito

Musulmai na son a amince da shari'ar musulunci a Osun
Kungiyar OSMC na son gwamna Adeleke ya amince da shari'ar musulunci a jihar Osun Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Musulmai daga sassa daban-daban na jihar sun yi dafifi a filin wasan ƙwallon ƙafa na Osogbo, inda ɗalibai suka gudanar da fareti na musamman.

Gwamna Adeleke ya samu wakilcin kwamishinan ayyuka na musamman, Mr BT Salam a wajen taron wanda sarakunan gargajiya da manyan baƙi suka halarta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ƙungiyar OSMC na son a amince da shari'ar musulunci a Osun

Olawuyi ya buƙaci gwamna Adeleke da ya amince da Shari'ar musulunci a jihar bisa tanadin kundin tsarin mulkin ƙasar nan wanda ya tabbatar da ƴancin yin addini ba tare da wata tsangwama ba.

Ya kuma buƙaci gwamnan jihar da ya ɗauki malaman Larabci da na Islamiyyah a makarantun jihar, inda ya bayyana cewa adadin yawan waɗanda ake da su makarantu sun yi kaɗan.

Alhaji Olawuyi ya kuma yi kira ga gwamnan jihar da ya farfaɗo da masana'antun da suka durkushe a jihar domin samarwa da matasa ayyukan yi.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Shugaba Tinubu Ya Sake Magana Mai Jan Hankali Kan Matsalar Tsaron Najeriya

Gwamna Adeleke Ya Nada Kwamishinoni a Jihar Osun

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Osun Ademola Nuruddeen Jackson Adeleke, ya nada kwamishinoni waɗanda zai yi aiki tare da su a gwamnatinsa.

Naɗin kwamishinonin na gwamna Adeleke dai na zuwa ne bayan ya shafe watanni tara akan karagar mulkin jihar Osun.

Gwamna Adeleke, wanda ya karɓi rantsuwar kama aiki ranar 27 ga watan Nuwamba, 2022, ya ɗauki tsawon lokaci yana tafiyar harkokin gwamnati ba tare da kwamishinoni da hadimai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel