Miji Ya Garzaya Kotu Kan Barazanar Kaciya Da Matarsa Ta Yi Ma Sa a Kano

Miji Ya Garzaya Kotu Kan Barazanar Kaciya Da Matarsa Ta Yi Ma Sa a Kano

  • Wani magidanci ya maka matarsa gaban kotun shari'ar Musulunci da ke zamanta a rijiyar Lemo Kano
  • Mijin ya nemi kotun ta dakatar da matar ta sa daga ƙoƙarin sabunta ma sa kaciya da ta yi iƙirarin yi
  • Ya ce ba su taɓa samun matsala da ita a baya ba, amma gashi yanzu tana neman yi ma sa ɗanyen aiki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Wani magidanci mai suna Malam Ali, ya garzaya kotun shari'ar Muslunci da ke zamanta a rijiyar Lemo, don neman dakatar da matarsa daga iƙirarin sabunta ma sa kaciya da ta yi.

Ya shaidawa kotun cewa matar ta sa ta dade tana faɗa ma sa cewa za ta yi ma sa kaciya, inda a yanzu haka ma ya ce ta sayo wuƙa mai kaifi don cika aniyarta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Malamar Da'awa Ta Fadi Cewa Ta Hango Peter Obi Ya Zama Shugaban Najeriya

Mata ta sha alwashin yi wa mijinta lafiya a Kano
Miji ya maka matarsa kotu kan yunkurin yi ma sa kaciya da ta yi. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Mijin ya ɗauke wukar da matar ta sayo

Mijin, wanda ya kasance mata biyu gareshi, ya bayyana cewa tun ranar da ta yi wannan iƙirarin ya daina barci da idanu biyu a duk lokacin da zai kwana gidanta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alƙalin da ke kula da koken da aka shigar Malam Sunusi Danbaba Daurawa, ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 4 ga watan Oktoba.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ɗage sauraron ƙarar, mijin ya bayyana cewa yanzu haka dai ya yi nasarar ɗauke wukar daga ɗakin matar ta sa, sai dai har yanzu hankalinsa bai kwanta ba.

Matar ta yi ikirarin sabuntawa mijin ka iya

Malam Ali ya kuma bayyana cewa bai san dalilin da ya sa matar ta sa ta yi hakan ba, saboda a cewarsa suna zaune lami-lafiya da ita.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito: Babban Dalilin Da Ya Jawo Wa PDP da Atiku Rashin Nasara Hannun Tinubu Ya Bayyana

Ya ƙara da cewa yana matuƙar ƙaunar matarsa, amma kuma ga abinda take shirin aikatawa, wanda ya sanyi shi kawo ƙararta gaban kuliya domin a tsayar da ita.

Manema labarai da suka yi kokarin jin ta bakin wannan mata kan abinda take shirin aikatawa, taki yadda ta yi hira da su.

Dan Najeriya ya gargadi masu barin matansu a gida su tafi Turai

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan gargaɗin da wani ɗan Najeriya mazaunin ƙasar waje ya yi wa magidanta masu barin matayensu a gida su tafi kasashen Turai.

Ya ce yin hakan yana da matukar hadari, domin kuwa mafi yawan matan ba sa iya riƙe amanar mazajen na su a lokacin da suka tafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel