Abba Gida Gida Ya Bayyana Naira Miliyan 854 Na Auren Zaurawa A Matsayin Tallafin Rage Radadi

Abba Gida Gida Ya Bayyana Naira Miliyan 854 Na Auren Zaurawa A Matsayin Tallafin Rage Radadi

  • Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir ya bayyana cewa auren zaurawa da ake shirin yi a jihar tamkar rage radadi ne
  • Ya soki wadanda ke korafi kan wannan mataki na gwamnatin jihar inda ya ce hakan babu wahalar da zai kara wa mutane sai dai rage musu
  • Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Bichi yayin da ya ke hira da Trust TV a yau Alhamis 14 ga watan Satumba

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da ware Naira miliyan 854 na auren zaurawa a matsayin tallafin rage radadi.

Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Bichi shi ya bayyana haka yayin hira da gidan talabijin na Trust a yau Alhamis 14 ga watan Satumba.

Abba Kabir ya ce auren zaurawa na daga cikin rage radadin wahala
Abba Gida Gida Ya Yi Magana Kan Ware Miliyan 854 Na Auren Zaurawa. Hoto: @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Meye Abba Gida Gida ya ce kan auren zaurawa?

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Babban Albishir Ga Yan Najeriya Kan Gwamnatin Tinubu, Ya Ce Romon Dadi Na Nan Tafe

Bichi ya ce auren zaurawan na daga cikin alkawuran da gwamnan ya yi kuma zai zamo kaman tallafin rage radadi ne ga mutane.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce ya na mamakin yadda mutane ke cewa hakan zai kara saka mutane cikin mayuyacin hali.

Ya ce:

"Ba na fahimtar dalilin da ake cewa wai aurar da marasa karfi zai kara saka su cikin wahala.
"Mun san nawa ake kashewa ayi aure, wasu iyalan ba su da halin aurar da 'ya'yansu duk da su na da manema.
"Wannan mataki zai iya zama kamar tallafin rage radadi ne a wurinsu, kuma hakan zai rage aikata laifuka wanda shi ne ya ke kara talauci."

Meye mutane ke cewa kan Abba Kabir na auren zaurawa?

Mutane da dama a jihar na sukar wannan mataki inda su ke cewa ta yaya za a kashe makudan kudade irin wannan a aure madadin inganta rayuwar al'umma.

Kara karanta wannan

“Idan Lasifika Ba Zai Yi Aiki Ba, Ta Yaya Abuja Za Ta Yi Aiki”: Wike Ya Yi Wa Jami’an FCTA Wankin Babban Bargo

A martaninshi, Bichi ya ce jihar ta fara raba tallafin rage radadi inda ya ce ba a yi adalci ba yadda gwamnatin Tarayya ta yi rabon ganin yadda su ke da jama'a a Kano.

Ya kara da cewa gwamnatin ta kafa kwamitin da zai kula da rabon kayan ba tare da matsala ba, Legit ta tattaro.

Mata sun hango 'yan majalisa a auren zaurawa

A wani labarin, wasu daga cikin jagororin matan Kwankwasiyya, sun yi magana a kan shirin auren zaurawa da gwamnatin jihar Kano ta dawo da shi.

Da ‘yan jarida su ka yi hira da Shafa’atu Ahmad a gidan rediyon Freedom, ta shaida cewa matan da za a aurar sun hango mazan da suke so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel