Gwamna Akeredolu Na Jihar Ondo Ya Sallami Dukkan Hadiman Mataimakinsa

Gwamna Akeredolu Na Jihar Ondo Ya Sallami Dukkan Hadiman Mataimakinsa

  • Alaka na kara tsami yayin da Gwamna Akeredolu ya kori dukkan hadiman mataimakinsa
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya shafe watanni ya na jinya a kasar Jamus
  • Kafin dawowarsa a wannan mako, an samu takun saka tsakanin mataimakin gwamnan da na kusa da gwamnan

Jihar Ondo - Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya sallami dukkan hadiman mataimakinsa, Lucky Ayedatiwa.

Korar hadiman na kunshe ne a cikin wata sanarwa ta bakin sakataren yada labaran gwamnan, Richard Olatunde a yau Talata 12 ga watan Satumba.

Akeredolu ya kori hadiman mataimakinsa
Gwamna Akeredolu Da Mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa. Hoto: Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Yaushe Akeredolu ya kori hadiman mataimakinsa?

Wannan na zuwa yayin da ake tunanin akwai takun saka tsakanin gwamnan da mataimakinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta tattaro cewa korar hadiman na daga cikin shirin wargaza dukkan mukamai a jihar.

Kara karanta wannan

Mataimakin Gwamnan Jam'iyyar APC Ya Yi Murabus Daga Muƙaminsa? Gaskiya Ta Bayyana

Bayan korar hadiman, an umarci ma'aikatar yada labarai ta ci gaba da kula da ayyukan ofishin mataimakin gwamnan.

Mataimakin gwamnan wanda shima ya na daga cikin masu neman kujerar gwamna a zaben da za a gudanar ya fara samun matsala da shugabannin jam'iyyar APC.

Meye martanin mataimakin Akeredolu kafin korar?

Da ya ke mayar da martani, Aiyedatiwa ya ce ba shi da wata matsala tsakaninshi da mai gidansa kamar yadda ake yadawa.

A cikin wata sanarwa, kakakinsa, Kenneth Odusola-Stevenson ya bayyana cewa babu wata kalar karairayi da zai sa ya juya wa uban gidansa baya.

Wannan sanarwa na zuwa ne sa'o'i kadan kafin Gwamna Akeredolu ya kori dukkan hadiman mataimakinsa ta bangaren yada labarai, Legit ta tattaro.

A cikin wata sanarwa, Akeredolu ya umarci dukkan wadanda abin ya shafa da su mika abubuwan gwamnati da ke tare da su zuwa ga sakataren din-din-din na ofishin mataimakin gwamnan.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fara Sakawa El-Rufai Bayan Nada Yaronshi Shirgegen Mukami, Bayanai Sun Fito

Gwamna Akeredolu Ya Dawo Najeriya Bayan Tsawon Lokaci Yana Jinya

A wani labarin, alamu sun nuna cewa gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya dawo gida Najeriya daga hutun jinya da neman lafiyan da ya tafi kasar Jamus.

Gwamna Akeredolu ya bar Najeriya zuwa kasar Jamus watanni da dama da suka gabata domin jinyar rashin lafiyar da ya ke fama da ita.

Rahonanni sun nuna cewa bayan shafe watanni yana jinya, gwamnan ya dawo gida Najeriya yau Alhamis, 7 ga watan Satumba, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel