“Aketi Na Nan Daram-Dam”: Hoton Gwamna Akeredolu Daga Gadon Asibiti Ya Bayyana

“Aketi Na Nan Daram-Dam”: Hoton Gwamna Akeredolu Daga Gadon Asibiti Ya Bayyana

  • Da alama Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya fara farfadowa daga halin rashin lafiya bayan wani bidiyo da hotonsa sun bayyana a ranar Juma'a, 21 ga watan Yuli
  • A yayin cikarsa shekaru 67 a duniya, matarsa, Betty Anyanwu-Akeredolu, ta saki hotonsu tare a wani asibitin kasar waje
  • Hoton shine karo na farko da gwamnan ke bayyana a soshiyal midiya tun bayan da ya mika ragamar shugabanci ga mataimakinsa tare da tafiyarsa jinya a watan Yuni

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Matar gwamnan jihar Ondo, Misis Betty Anyanwu-Akeredolu, ta saki hoton farko na mijinta da ke fama da rashin lafiya, Gwamna Rotimi Akeredolu a sakon murnar zagayowar ranar haihuwarsa karo na 67.

Kamar yadda Legit.ng ta gani a Facebook, matar gwamnan na Ondo ta wallafa hoton ne a ranar Juma'a, 21 ga watan Yuli tare da taken, "Aketi na nan daram-dam! Nasara a garemu!"

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Fitaccen Basarake Mai Daraja a Najeriya Ya Mutu a Asibiti

Gwamna Akeredolu tare da matarsa
“Aketi Na Nan Daram-Dam”: Hoton Gwamna Akeredolu Daga Gadon Asibiti Ya Bayyana Hoto: Betty Anyanwu-Akeredolu
Asali: Facebook

Wannan shine karo na farko da ake ganin gwamnan wanda ke fama da rashin lafiya a soshiyal midiya tun bayan da ya mika harkokin shugabanci ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, a watan Yuni kafin ya tafi jinya.

Kamar yadda jaridar yanar gizo na SaharaReporters ta rahoto,Akeredolu ya tafi kasar waje jinya sakamakon cutar kansar jini (leukaemia).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kuma tattaro cewa gwamnan bai iya sa hannu a takardun ba kafin barinsa kasar zuwa jinya saboda yanayin rashin lafiyarsa.

Yanayin da yake ciki ya kuma yi sanadiyar haramta wayoyi a kusa da shi domin hana yada hotunan rashin lafiyarsa a kan intanet.

Gwamnan Rikon Kwarya Na Jihar Ondo Ya Yi Karin Haske Kan Rashin Lafiyar Gwamna Akerdolu

A gefe guda, Legit.ng ta kawo a baya cewa Lucky Orimisan Aiyedatiwa, gwamnan riƙon ƙwarya na jihar Ondo a ranar Talata, 11 ga watan Yuli, ya bayyana cewa ana yaɗa ƙarya da ƙarairayi kan haƙiƙanin halin rashin lafiyar da gwamna Rotimi Akeredolu yake ciki.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Tsare Wani Matashi Dan Kwaya Da Ake Zargin Ya Shake Wuyan Mahaifiyarsa Har Lahira

Legit.ng ta rahoto cewa Aiyedatiwa ya zama madadin gwamnan ne bayan ya tafi neman magani a ƙasar waje.

Da yake magana kan rashin lafiyar gwamnan, Aiyedatiwa ya bayyana cewa ya tattauna da Akeredolu a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel